Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar Da Sabbin Kayayyakin Koyon Harkar Lafiya A Makaratun Unguwar Zoma 2.
- Katsina City News
- 25 Nov, 2024
- 271
Daga Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times.
A ranar Litinin 25 ga watan Nuwamba 2024, gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda, ta kaddamar da sabbin kayayyakin zamani domin inganta karatun harkar lafiya a Makarantun unguwar zoma a Katsina da Malumfashi.
Alhaji Umar Mammada mai ba gwamna shawara kan makaratun kiwon lafiya, tare da PS Hajiya Safiya Yamel, da kuma Shugaban makarantun kiwon harkar lafiya na unguwar zuma, Dr. Aminu Bello Abdullahi ne suka jagoranci kaddamar da sabbin kayayyakin.
Kayayyakin sun hada da mutum-butumi wanda ke sarrafa kansa wajen koya wa dalibai yadda ake bada agaji lokacin da mace za ta haihu, da kuma sabbin Gadaje da sauran abubuwa wadanda suke taimaka wa dalibai wajen koyon harkar lafiya.
A jawabin da ya gabatar a wajen kaddamar da kayayyakin, shugaban makarantun unguwar zoma na garin Katsina, Dr. Aminu Bello Abdullahi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda gwamnati ta bayar da wannan tallafin, inda ya bayyana cewar tsawon shekaru 64 da bude makarantun ba a taba samun gwamnatin da ta bayar da kayayyaki kamar wadannan ba, sai a wannan gwamnatin.
Ya ce, wadannan kayayyaki ne na zamani sun dace da duk wasu makarantun unguwar zoma, kima sun dace da yanyin da za a koyar da daliban da su.
Ya kara da cewar, za su kasabta kayayyakin gida biyu; za a kai ɗaya a makarantar unguwar zoma ta cikin garin Katsina, a yayin da dayan kuma za a kai shi a Makarantar unguwar zoma ta karamar hukumar Malumfashi.
A yayin da yake jawabi a wajen kaddamarwar, mai ba gwamna sharawa kan makaratun kiwon Lafiya, Alhaji Umar Mammada ya yaba wa gwamnatin jihar bisa ayyukan da take yi a fadin jihar, musamman wadanda suka shafi inganta ilimin harkar lafiya.
Mammafa, ya kuma jan hankalin dalibai da za su amfana da wadannan kayayyaki a kan su dage wajen ganin sun koyi abin da ake kira "Mash" a turance, sannan kuma su kula da kayayyakin domin wadanda za su zo bayansu su ma su amfana.