Gwamnatin Jihar Katsina Ta Jaddada Kudirin Bunkasa Ilimi a Taron Yaye Dalibai Na Jami’ar Dutsin-Ma
- Katsina City News
- 03 Nov, 2024
- 267
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
A yayin taron yaye dalibai karo na tara na Jami’ar Dutsin-Ma da aka gudanar a ranar 2 ga Nuwamba, 2024, a filin wasanni na jami’ar, Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da aniyarta na fadada damar ilimi ga matasa. A cikin jawabinsa a madadin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, ya bayyana irin jarin da gwamnatin ke zuba a bangaren ilimi da kuma dabarun da ake dauka don inganta samun damar ilimi mai zurfi a fadin jihar.
Faskari ya jaddada kudirin gwamnatin a karkashin shirin “Gina Makomarku,” wanda ya bayar da tallafin karatu fiye da naira biliyan uku daga shekarar 2017 zuwa 2022, tare da shirye-shiryen karin kudade don tallafin shekarar 2024. Bugu da kari, an daukaka Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi zuwa cikakkiyar ma’aikata, wanda zai tabbatar da kula da manyan makarantu, makarantu na sana’o’i, da cibiyoyin koyon sana’o’i.
A bangaren kiwon lafiya da fasaha, Faskari ya sanar da cewa an bai wa dalibai 40 tallafin karatu na likitanci a kasar Masar, yayin da wasu 67 suka samu tallafi domin nazarin fasahar wucin-gadi (artificial intelligence). Gwamnati ta kuma shirya daukaka Cibiyar Fasaha da Gudanarwa ta Katsina zuwa jami’a, a matsayin wani mataki na kara gina kwararrun ma’aikata a yankin.
A karshen jawabinsa, Faskari ya yi kira ga daliban da su ci gaba da koyon ilimi a rayuwarsu tare da tabbatar musu da ci gaba da samun goyon bayan gwamnati a bangaren bunkasa ilimi.
Mataimakin Shugaban Jami’ar Dutsin-Ma, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, ya taya dalibai fiye da 4,500 murna, ciki har da wadanda suka sami matsayin First Class 44. Ya yi kira ga daliban da su kasance masu jajircewa da gaskiya a aikinsu, tare da gode wa manyan baki, malamai, da dukkan ma’aikata bisa goyon bayansu ga ci gaban jami’ar don tallafa wa ci gaban kasa.
A wannan shekara, jami'ar ta karrama fitattun mutane da digirin girmamawa saboda gudunmawar da suka bayar a bangaren ilimi, hidimar jama’a, da ci gaban kasa. Daga cikin wadanda aka karrama akwai Senator Oluremi Tinubu, Uwargidan Shugaba Bola Tinubu, Kakakin Majalisar Dattijai Sanata Akpabio, Hon. Abubakar Abban Bichi da Senator Aliyu Magatakarda Wamakko, Daga jihar Sokoto.
Nasarorin da suka cimma an bayyana su a matsayin abin koyi ga daliban da aka yaye.
A madadin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohamed, Mataimakin Shugaban Jami’ar Dutse, ya yabawa Gimbiya Oluremi Tinubu bisa goyon bayan da take ba wa jami’ar, musamman ta hanyar shirye-shiryen tallafawa dalibai mata ta hanyar tallafin karatu da kuma kafa asusun tallafi. Yayin da yake jaddada nasarorin da aka samu daga shekarar 2020 zuwa 2024, Mohamed ya bayyana kalubalen tsaro da jami’ar ke fuskanta, amma ya jaddada cewa jami’ar za ta ci gaba da jajircewa wajen samun ci gaba.
Chancellor na makarantar, Sarkin Opobo, King Dandeson Douglas Jaja, wanda ya halarci taron yaye daliban, ya yaba wa ci gaban jami’ar tare da bayyana alfaharin da yake da shi ga daliban da aka yaye. Ya yi kira ga daliban da su zama wakilai masu daraja ga jami’ar, tare da jinjina musu bisa jajircewa da himmar da suka nuna yayin da suke shirin fuskantar sabbin kalubale a rayuwarsu ta sana’a.