RIKICIN PDP A KATSINA: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Zaben Shugabancin Jam'iyyar
- Katsina City News
- 28 Oct, 2024
- 239
Katsina Times
Babbar kotun jihar Katsina ta dage shari’ar rikicin zaben jam’iyyar PDP zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci kan karar da wani bangare na jam’iyyar ya shigar, yana kalubalantar yadda aka gudanar da zabukan jam'iyyar.
Idan ba a manta ba, bangaren jam'iyyar da Sanata Yakubu Lado ke jagoranta ne ya gudanar da zabukan da suka samar da sabbin shugabannin jam'iyyar daga matakin gunduma har zuwa na jiha.
Sai dai wani bangare na jam’iyyar karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Mustafa Inuwa, da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun shigar da kara a babbar kotun jihar, suna kalubalantar sahihancin gudanar da zabukan.
Lauyan wadanda ake kara ya gabatar da bukatar kotun ta yi watsi da karar bisa hujjar cewa rikicin cikin gida ne na jam’iyyar wanda bai kamata kotu ta shiga ba.
Bayan sauraron jawabai daga lauyoyin bangarorin biyu, alkalin kotun, Mai shari’a Abbas Bawale, ya dage karar zuwa 29 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci.
A yayin wani taron manema labarai bayan zaman kotun, lauyan bangaren jam'iyyar PDP tsagin Lado Danmarke, Barr. Isaac Nwachukwu, ya bayyana cewa zabukan jam’iyya na cikin gida ne, don haka bai dace a shigar da shi gaban kotu ba. Ya ce, "Mu na ganin cewa rikicin cikin gida ne wanda kamata ya yi jam’iyyar ta warware a cikin kanta ba tare da kotu ta tsoma baki ba."
Shi ma lauyan wadanda suka shigar da kara, Barr. Mustafa Shitu Mahuta, ya bayyana cewa sun kawo kara ne domin kalubalantar yadda aka gudanar da zabukan PDP daga matakin jiha zuwa gunduma. Ya ce, "Bangare daya ne ya mamaye dukkanin tsare-tsaren zabukan ba tare da baiwa sauran mambobin jam’iyyar damar shiga zaben ba. Don haka mu na neman kotu ta rushe zaben tare da umartar a sake sabon zabe mai inganci."