ILIMI: Gidauniyar Oando Zata Kammala Gyaran Makarantu a Katsina da Daura Kafin Karshen Watan Disamba
- Katsina City News
- 22 Oct, 2024
- 421
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Auwal Isah (Katsina Times)
Gidauniyar Oando ta sha alwashin kammala gyaran makarantu a Katsina da Daura kafin mako na biyu na watan Disamba, kamar yadda aka bayyana a wata ganawa ta manyan jami’ai a jihar Katsina. Gidauniyar, wacce ta dade tana bada tallafi wajen inganta ilimi a yankin, na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen gyare-gyare don inganta ginin makarantu da yanayin koyarwa a Makarantu Firamare da Sakandare.
A yayin ganawar, Kwamishiniyar Ilimin Firamare da Sakandare, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta bayyana godiyarta ga Gidauniyar Oando bisa irin gudunmawar da suke bayarwa ga bunkasar ilimi a jihar. Ta ce, "Mun ziyarci makarantar Family Support a Daura, inda kamfanin ya amince da gyaran makarantar firamare, sashin yara ƙanana, da wuraren wasanni. Yanzu haka suna ci gaba da aikin irinsa a Katsina, inda suka kammala kimanin kashi 60% na aikin."
Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, shima ya yabawa kokarin Gidauniyar Oando, yana mai cewa gidauniyar ta kasance abokiyar huldar gwamnati wajen magance kalubalen ilimi. Ya ce, “Gwamnati ba za ta iya komai ita kadai ba. Shigar irin wadannan kungiyoyi masu kishin al’umma kamar Gidauniyar Oando na taimakawa wajen cike gibin da ake da shi wajen samar da ingantaccen ilimi ga kowa ba tare da bambanci ba."
Manajan Shirin na Gidauniyar Oando, Tonia Uduimoh, ta bayyana karin haske game da ayyukan gidauniyar. Ta ce gidauniyar ta dade tana bada tallafi a fannin ilimi a jihar Katsina, tun daga makarantar General Muhammadu Buhari a Daura. “Manufarmu ita ce rage gibin da ake da shi a ilimin yaran da ke cikin yankunan da ba su samu ci gaba sosai ba. Muna aiki a jihohi 23 a fadin kasar nan, ciki har da Katsina, inda muka taimaka wa makarantu guda bakwai,” inji ta.
Haka kuma, Uduimoh ta tabbatar da cewa bayan gudanar da bincike, gidauniyar ta amince da gyara makarantu a Family Support Primary da Nursery a Katsina da Daura. “Burinmu shi ne tabbatar da cewa yaran da ke makarantu na gwamnati sun samu irin damar da yaran da ke makarantu masu zaman kansu ke samu, ba tare da la’akari da matsayin tattalin arzikinsu ba,” ta kara da cewa.
Ana sa ran kammala ayyukan gyaran makarantu nan da watan Disamba, wanda zai kara kawo ingantaccen ilimi ga yaran Katsina da Daura.