ZARGIN RASHIN GASKIYA A TALLAFIN GWAMNATI GA MUTANEN DAN MUSA ...Duk wanda aka ba saida ya bada wani kaso
- Katsina City News
- 11 Oct, 2024
- 426
"Duk wanda aka ba, sai da ya bada wani kaso,"
...inji wadanda muka tattauna da su.
"Bani ciki, kuma ban san maganar ba," ...inji shugaban karamar hukumar Dan Musa.
Muazu Hassan Katsina Times
Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da wani shiri na tallafi don tausayawa wadanda ibtila'in barayin daji ya shafa. An tsara shirin ne don saukaka wa mutanen da suka shiga cikin mawuyacin hali sakamakon wannan matsala. Wannan tallafin da gwamnatin Dikko Radda ta bullo da shi ya samu yabo daga wadanda abin ya shafa, inda da yawa daga cikinsu suka nuna jin dadin su, suna cewa tallafin ya taimaka wajen farfadowar rayuwarsu.
A cikin watan Satumba, mutanen karamar hukumar Dan Musa sun samu kashin farko na tallafin. An gudanar da rabon ne a tsohon gidan gwamnatin Katsina, karkashin ofishin mai bai wa gwamnatin Katsina shawara kan harkokin wadanda barayin daji suka yi wa barna.
Amma, jaridar Katsina Times ta samu korafe-korafe daga wasu mutanen da aka bai wa tallafin, suna zargin an rika amsar wani kaso daga duk abin da aka ba su. An gano cewa tallafin yana rarrabuwa bisa asarar da mutum ya yi, amma wasu sun ce ana bukatar su bayar da kashi goma cikin dari, wasu kuma har kashi ashirin. Haka kuma, akwai wurare da aka yi rabon yanda ya kamata.
Jaridar Katsina Times ta samu jerin sunayen wasu daga cikin wadanda aka bai wa tallafin a mazabar Dan Musa B da Maidabino B. Wadanda aka tattauna da su sun kara tabbatar da zargin, inda suka ce an gargade su kada su bari maganar ta fito fili, saboda tsoron a dakatar da tallafin gaba daya idan ta fito.
Wake Amsar Kudaden?
Binciken Katsina Times ya gano cewa kudin tallafin ana amsar su daga wadanda aka bai wa, amma ba a tabbatar da wanda ya sa aka rika amsar kudaden ba, ko kuwa wa suka yi rabon su tare da shi.
Jaridar Katsina Times ta tuntubi shugaban karamar hukumar Dan Musa, Alhaji Sanusi Abbas Dangi, wanda ya ce ba shi da hannu a cikin rabon tallafin, kuma bai san komai ba. Sai dai ya nuna goyon bayan sa ga bincike mai zaman kansa domin gano gaskiya.
Hakazalika, Katsina Times ta tuntubi Alhaji Saidu Ibrahim Danja, mai ba gwamnatin Katsina shawara kan harkokin wadanda ibtila'in barayin daji ya shafa, wanda ya musanta sanin komai game da zargin. Ya kara da cewa, idan akwai wani abu da ya faru, bai da masaniya kuma bai da hannu a ciki.
Dan majalisar dokokin jihar Katsina daga karamar hukumar Dan Musa, Alhaji Aminu Garba, shima ya ce ya ji wannan jita-jitar, amma ya karyata ta. Ya ce duk wanda yake ikirarin ya bada kudi, ya fito ya bayyana wa ya ba. Ya kuma bayyana cewa taimakon jama'a kawai suka yi, ba tare da samun wani sakamako ko cin amana ba.
A karshe, wani Maigari da ya nemi a boye sunansa ya ce gwamnati ta kara sanya ido kan wadanda ta bai wa amanar raba kudaden, domin magance irin wannan matsalar nan gaba.
Katsina Times
www.katsinatimes.com
Taskar Labarai
www.taskarlabarai.com
07043777779 | 08057777762