Ƴan ta'addar da suka tsere daga Zamfara na yi wa Kano barazana
- Katsina City News
- 11 Oct, 2024
- 360
Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa-ido sosai a birnin Kano, bayan da wani rahoton da hukumomin tara bayan sirri suka gano cewa yanzu ɗimbin ƴan bindiga sun tsere daga Zamfara inda suke fakewa a cikin birnin wanda shi ne mafi girma a arewacin kasar.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ne ya sanar da hakan, bayan da ya samo kwafin wasikar da hukumomin tara bayanan sirri daga Zamfara suka tura wa takwarorinsu da ke Kano.
A cewar AFP, tun a ranar Litinin da ta gabata ne aka gabatar wa gwamnan jihar Kano da wannan rahoto, da ke cewa mafi yawan ƴan bindigar tuni suka mallaki gidaje a cikin birnin Kano, yayin da wasu ke fakewa a unguwannin Rijiyar Zaki, Tudun Yola, Ja'en, Ɗorayi Babba, Rijiyar Lemo da kuma Ƴan Awaki.
Bisa ga dukan alamu, rahoton ya ce mafi yawan ƴan bindigar sun nemi mafaka a birnin Kano ne saboda tsanantar hare-hare da jami’an tsaro ke kai musu a cikin ƴan kwanakin nan, yayin da wasu suka mallaki gidajen tsawon shekaru a birnin a daidai lokacin da suke taimaka wa ƴan bindigar da ke gudanar da ayyukan tsagarenci a jihohin Zamfara, Katsina da kuma Kaduna.
Wasu majiyoyi biyu na tsaro, sun tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran AFP da cewa rahoton ya shiga hannuwansu, yayin da wata majiyar ke cewa yanzu tana aiki tukuru domin zaƙulo su a cikin gaggawa.
To sai dai majiyar na cewa yanzu haka jami’an tsaro na aiki ne a asirce domin ka da jama’a su shiga hali na firgita.