SOKE AIKIN HANYA A KATSINA: MATAFIYA, AL'UMA DA KUNGIYOYIN FARAREN HULA SUN YI ALLAH-WADAI
- Katsina City News
- 07 Oct, 2024
- 565
A farkon shekarar nan ne gwamnatin tarayya ta bada aikin hanyar Marabar Kankara zuwa Katsina mai tsawon kilomita 170 ganin yadda hanyar ta lalace shekaru talatin bayan gina ta.
Sai dai a dai-dai lokacin da dan kwangilar ya kama aikin hanyar gadan-gadan, sai gashi an dakatar da aikin ba tare da an bayyana dalilan dakatarwar ba.
Sai a ranar Lahadin nan ne sabbin bayanai suka fito daga bakin mataimaki na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, wanda ya bayyana cewa Gwamna jihar, Malam Dikko Radda, shi ya roki shugaban kasa a dakatar da aikin hanyar.
Masari ya bayyana haka ne a taron rabon tallafin shinkafa wacce gwamnatin tarayya ta aiko a raba ma mabukata a jihar Katsina.
Yace "akwai aikin hanya wacce ta taso daga Marabar Kankara zuwa Kankara zuwa 'Yantumaki zuwa Dutsinma zuwa Kurfi zuwa Katsina.
"An bayar da aikin, amma sai aka yi rashin sa'a domin an ajiye kwarya a inda ba gurbinta ba.
"Saboda haka Gwamnan Jihar Katsina ya je ya sami Shugaban kasa yace a soke wannan aikin a sake ba mutumin da muke da tabbacin cewa zai yi aiki nagartacce", inji Ibrahim Masari.
Sai dai kuma bayan wannan fallasa Gwamna Radda yana cigaba da shan suka daga matafiya dake bin hanyar da kungiyoyin fararen hula da mazauna garuruwa da kauyukan da ke kan hanyar wacce ta hada kananan hukumomi bakwai
Har ila yau ganin cewa Sanata Yakubu Lado, dan takarar Gwamnan jihar Katsina karkashin inuwar jam'iyyar PDP a manyan zabukan bara, shi ya amso aikin hanyar yasa al'uma ke cewa an soke aikin ne saboda dalilan siyasa.
Wani direban motar kasuwa mai suna Haruna Abdu, ya koka da cewa duk da tsadar mai, direbobi sai sun zagaya ta doguwar hanya kafin su isa Katsina.
“Ga mu direbobin da ke fitowa daga Funtua ko Zaria, hanyar Kankara ita ce hanya mafi sauri, amma ba a tashi dakatar da aikin hanyar ba sai da aka kankare ta.
“Yanzu dole mu ke bi ta Musawa ko ta Gidan Mutum Daya idan za mu zo Katsina.
“Sakamakon tsadar man fetur, masu motocin kasuwa da masu motocin kansu dole su kara kashe kudin mai saboda wannan zagayen da suke yi” in ji Malam Haruna.
Su kuwa mazauna kauyukan da ke kan hanyar Marabar Kankara zuwa Katsina, sun ce dakatar da aikin hanyar ta kara tsananta rashin tsaro a yankin.
Dan-Gambo Faruku, mazaunin garin Burdugau, ya bayyana yadda garkuwa da mutane da fashin daji suka kara ta’azzara sakamakon dakatar da aikin hanyar.
Malam Dan-Gambo ya ce “daga lokacin da aka dakatar da aikin zuwa yanzu, an sace mutane da dama, an kuma kai hare-hare a kauyuka da dama.
“An kai hari yafi sau-a-kirga a tsakanin Burdugau zuwa Yargoje zuwa Kuka-sheka zuwa Danmarke zuwa Kankara.
“Saboda an rufe hanyar, jami’an tsaro ba za su iya kawo mana dauki cikin gaggawa ba, kauyukanmu sun zama ihunka banza.
“Hakazalika, saboda motoci sun daina bin hanyar, yanzu hanyar ta zama shiru kamar makabarta, shi ya sa ‘yan bindiga ke kawo mana hari a ko da yaushe suka ga dama.
A barayi guda kuma, kungiyoyin fararen hula a jihar Katsina sun yi Allah-wadai da matakin da Gwamna Dikko Radda ya dauka na zuga Shugaba Tinubu ya soke aikin hanyar saboda dalilan siyasa.
Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi wanda shine shugaban Kungiyar Mutanen Arewacin Najeriya, reshen jihar Katsina, ya bayyana dakatar da aikin a matsayin abin takaici.
“Wannan hanyar muhimmancinta ya fi karfin a bari bambamcin siyasa yasa a dakatar da aikinta tana.
"Da aka fara aikin al'uma suna ta murnar musamman ganin cewa aiki ne da Shugaba Buhari ya gaza bayarwa tsawon shekara takwas da yayi a karagar mulki.
"Sai dai yayi ta waka da daukar alakawura kamar yadda yayi alkawarin gina hanya daga Kano zuwa Katsina, sai ga shi har yayi shekara takwas ya sauka ba a kammala aikin ba.
"Yau sai gashi Shugaba Bola Tinubu ya bada aikin wannan hanyar ta Marabar Kankara zuwa Katsina, amma sai gashi wai Gwamna ne yaje yace a soke aikin, wannan abin takaici ne kuma abin kunya,
"Duk wani dalilin da gwamna zai bayar wallahi ba dalili bane, ko dalili na siyasa ko na son zuciya, ko kuma cewa wai an bada aikin ga wanda bai dace ba, wannan wasa ne da kwakwalwar al'umar jihar Katsina", inji Jamilu Charanchi.
Sauran masu ruwa da tsaki sun bayyana damuwarsu ne kan yiwuwar kara bada aikin ganin yadda bisa ala'ada ake samun jinkiri wajen bada kwangila da fitowar kudin kwangilar.
Malam Aliyu Yantumaki daga karamar hukumar Danmusa na daga cikin wadanda suka bayyana wannan damuwar.
Ya ce "a gwamnatance, samun kwangilar babban aiki irin wannan yana da wahala matuka.
"Dole sai an bi matakai masu tsawo kuma ko an samu kwangilar, kafin a fitar da kudin aikin sai an dauki lokaci mai tsawo.
"Shi ya sa mu ke da fargabar cewa da kyar a cigaba da wannan aikin, sai dai illa ma sha Allahu", inji Yantumaki.
A barayi guda kuwa, Gwamna Dikko Radda ya bayyana ma mahalarta taron rabon tallafin shinkafa daga gwamnatin tarayya cewa ya gana da Shugaba Bola Tinubu inda ya nema ma jihar Katsina wasu manyan aiyukan hanya daga gwamnatin tarayya.