Tashin Gobara A Fadar Gwamnatin jihar: Gwamna Radda Ya Kafa Kwamitin Bincike
- Katsina City News
- 02 Sep, 2024
- 494
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
Wata gobara ta tashi a yau a Gidan Gwamnatin jihar Katsina wato "Muhammadu Buhari House" wani bangare na ofishin Gwamnan Jihar Katsina, inda ta lalata Karamin Ofishin Gwamnan, Ma’aikatan kashe gobara daga hukumomin tarayya da na jiha sun yi nasarar shawo kan wutar kafin ta bazu zuwa sauran sassan ofishin.
A wata takarda mai dauke da saka Hannun Abdullahi Aliyu Yar'adua, Daraktan Yada Labarai na Sakataren Gwamna, Malam Dikko Umaru Radda ya kafa kwamitin bincike don gano musabbabin wannan gobara, tare da ba da wasu sharuddan da za su jagoranci binciken:
- Gano musabbabin tashin gobarar
- Tantance girman asarar da aka yi
- Gano duk wata gazawa da ta haifar da wannan lamari
- Ba da shawarar matakan da za a dauka don hana faruwar irin wannan a nan gaba
- Samar da wasu karin shawarwari da ake ganin sun dace
An ba wa kwamitin, wanda ya kunshi manyan jami'an gwamnati, mako guda don gabatar da rahoton su, tare da ba su damar hada karin mambobi idan bukatar hakan ta taso.
Gwamna Radda ya bayyana cikakken kwarin guiwa ga kwamitin da aka kafa, yana mai cewa za su gudanar da cikakken bincike tare da samar da shawarwari masu amfani don hana faruwar irin wannan a nan gaba.