TATSUNIYA TA 48; Labarin Nasiru Da Nasiru
- Katsina City News
- 01 Sep, 2024
- 503
Ga ta nan, ga ta nanku.
A garin Mazarkwaila an yi wani yaro mai suna Nasiru, ɗan Sarkin Zaki. Shi Nasiru yana da wani aboki mai suna Nisiru. Ana kiran baban Nasiru "Sarkin Zaki" ne saboda ya fi kowa iya yin kayan zaki a garinsu. Duk lokacin da Nisiru ya zo wajen Nasiru, sai su tafi cin zuma tare; watau su kona itace domin hayakin ya kori kuda, sannan su kwashi zuma da ruwan zuma. Haka suke yi kullum.
Ana nan, ana nan, sai mahaifiyar Nasiru ta rasu. Da zarar ta rasu, sai kishiyar uwarsa ta shiga ba Nasiru wuya. Duk da haka, ɗan kishiyar, mai suna Aliyu, yana son Nasiru sosai, kuma ba ya nuna masa kiyayya ko kaɗan. Wata rana, sai Aliyu ya ce wa Nasiru da abokinsa, "Yau zan raka ku cin zuma."
Nasiru ya ce masa, "Ni fa ina tsoro, kada mahaifiyarka ta yi faɗa."
Sai Aliyu ya ce, "Ba komai, ba za ta yi faɗa ba sam-sam." Daga ƙarshe dai, Nasiru ya amince zai tafi da Aliyu.
A lokacin da Nasiru da Aliyu suke wannan magana, wata mata magulmaciya ta ji su, sai ta je ta shaida wa mahaifiyar Aliyu cewa Nasiru da Nisiru za su ja ɗan ta cikin daji su halaka shi.
Da jin wannan labari, sai mahaifiyar Aliyu ta ce wa matar, "Yanzu yaya za mu yi?"
Matar mai zuga ta ce, "Akwai wani hatsabibin boka wanda zai ba mu maganin da zai kashe Nasiru kawai mu kawar da shi."
Wannan shawara ta tsorata mahaifiyar Aliyu, sai ta ce, "A'a, ni fa ina tsoron kashe mutum."
Sai matar nan ta ce, "Idan ba ki kashe yaron nan ba, zai fi ɗan ki arziki domin yana da kashin arziki."
Da jin wannan gurguwar shawara, sai mahaifiyar Aliyu ta ce, "To, shi ke nan, mu je."
Uwar Aliyu da mai zuga suka je gidan boka suka yi masa bayani. Nan take kuwa boka ya ba su magani, ya ce su zuba a nono. Ya tabbatar musu cewa idan Nasiru ya sha, zai mutu. Suka dawo gida, uwar Aliyu ta ajiye fura da nonon da aka zuba wa magani a gindin randa, ta ɗanta Aliyu kuma ta ajiye masa tasa a kan randar.
Da Nasiru da Aliyu suka shiga gida, aka nuna wa kowa furarsa. Nasiru ya ɗauko tasa daga gindin randa, ya fara sha, amma sai ya lura uwar Aliyu tana kallonsa tana yi masa lara'a tare da wasa da dariya. Ganin haka, sai ya ce mata zai fita waje ya sha. Da ya fita waje, sai ya ba wani ɗan akuya furar kaɗan. Da nan take dan akuyan ya fadi matacce.
Da Nasiru ya ga haka, sai ya yi rami ya binne ragowar furar, ya kwanta kamar ya mutu. Jim kaɗan, sai ga mahaifiyar Aliyu ta leƙo ta ga Nasiru a kwance kamar ya mutu. Ba ta san sanda ta yi subur da baki ba cikin murna ta ce, "Yawwa, madalla! Tun da aka haifi yaron nan nake neman yadda zan gama da shi, ban sami nasara ba sai yanzu. Ba shakka wannan boka hatsabibi ne, na gode masa."
Tana cikin wannan murna, idanunta a rufe, ta ɗauki Nasiru ta kai shi bayan gari ta jefar; ko tunanin rufe gawarsa ba ta yi ba saboda tsananin kiyayya. Shi kuma Aliyu, ɗan uwan Nasiru, sai ya nemi uwar ta gaya masa inda yake. Da ƙyar dai ta yi masa bayanin inda yake. Sai Aliyu ya fita nemansa, ya ci sa’a kuma ya rera wata waka a kusa da inda aka jefar da shi:
"Nasiru, Nasiru, Nasiru,
Nasiru ɗan Sarkin Zaki,
Nasiru tashi mu je shan zaki.
Nasiru ya bar duniya,
Nasiru ya tafi lahira."
Duk da cewa Nasiru yana kusa da Aliyu, bai mayar masa da wannan waka ba. Sai Aliyu ya koma gida cikin matsanancin tashin hankali. Har ma dai ya ce wa uwar shi fa ba zai ji daɗin zaman duniya ba muddin ba ya ganin Nasiru.
A wannan lokaci, abokin Nasiru, watau Nisiru, shi ma ya shiga cikin damuwar rashin ganin abokinsa. Shi kuma ya sami uwar Aliyu ya ce mata:
"Mamayo, mamayo, mamayo,
Nasiru ya bar duniya,
Nasiru ya tafi lahira."
Zuciyarsa cike da bakin ciki, ya kama hanyar daji. Yana cikin tafiya sai ya ga wani mutum a zaune ya gama kai da gwiwa. Sai ya matsa kusa da shi ya ce, "Bawan Allah, me ya same ka haka?"
Mutumin ya ɗago kansa, sai ga shi abokinsa Nasiru ne.
Hankalin Nisiru ya kwanta, suka sami wuri suka zauna. Bayan sun yi 'yar hira, sai suka yanke shawarar barin garin don gudun mugun halin uwar Aliyu. Amma abokin nasa sai ya ce da shi, "Haba mutumina, kada ka ji tsoron komai. Ni ne Nasiru."
Sai suka tafi wani gari mai babbar kasuwa da filaye masu kyau, ga dausayi. A can suka shiga neman abin kansu. Kafin shekara ta cika, kowannensu ya mallaki dukiyar da ba a jima an ga mai kama da ita ba.
Wata rana bayan kusan shekara biyar, Nasiru da abokinsa suna cikin wata tafiye-tafiye, sai suka yanke shawarar cewa ya kamata su koma gida.
Nan da nan suka tattara dukiyarsu suka ɗora wa rakuma, suka tafi da ita garinsu. Nasiru ya tarar da uwar Aliyu tana cikin mummunan talauci, ga tsufa ya kama ta. Kanensa Aliyu kuma ya zama bawa a gidan wani mai arziki. Nan take, Nasiru ya ba ta dukiya mai tarin yawa.
Da hakan, uwar Aliyu ta shiga jin daɗi, ba da dadewa ba ta murmure. Nasiru kuma ya kawo jari mai yawa ya ba kanensa Aliyu. Shi da abokinsa kuma suka shirya suka koma wurin sana'arsu.
Duk sanda uwar Aliyu ta zauna, sai ta shiga tunanin irin muguntar da ta shirya wa Nasiru, da kuma irin alherin da ya yi mata. Sai ta yi da-na-sani, ta roƙi gafararsa, ya yafe mata.
Abubuwan da Labarin Yake Koyarwa:
1. Ba a rama alheri da mugunta.
2. Duk wanda ya bi shawarar magulmaci zai tsinci kansa cikin nadama da da-na-sani.
3. Mai hankali ba ya rama mugunta da sharri sai da alheri.
(Daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman)