Barayin Daji Sun Kai Hari Mai Tsanani a Garuruwan Shirgi da Kunya, Sun Sace Mutane da Dabbobi
- Katsina City News
- 20 Aug, 2024
- 341
Katsina Times
Barayin daji sun kai hari mai tsanani a garuruwan Shirgi da Kunya, yankin karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, inda suka sace mutane da dabbobi da dama. Wannan hari ya ƙara tsananta rashin tsaro da ya addabi yankin.
Wakilan Jaridar Katsina Times sun tattauna da mazauna garuruwan Shirgi da Kunya, inda suka tabbatar da cewa harin ya faru ne a ranar Lahadi, 18 ga Agusta, 2024, da misalin ƙarfe 11:59 na dare. Barayin sun kutsa cikin garuruwan suna harbin kan mai uwa da wabi, inda suka yi sanadiyar mutuwar wani mutum mai suna Amadu Siru.
A Shirgi, an sace mutane 35 daga gidaje daban-daban, ciki har da iyalan marigayi Amadu Siru guda huɗu. Haka zalika, an sace mutane bakwai daga gidan Malam Sada, mutane bakwai daga gidan Ibrahim Namaituwo, mutane huɗu daga gidan Malam Samaila, da mutane uku daga gidan Malam Muddaha, tare da wasu mutanen da dama.
A garin Kunya kuwa, barayin sun sace mutane 18 tare da dabbobi 52, ciki har da shanu 12 da tumaki 40. Wannan hari ya zo ne bayan wani hari makamancin haka da aka kai a kauyen Kurna cikin makon da ya gabata, inda aka kashe mutane biyu, sannan aka sace mutane 18 da har yanzu ba a ga su ba.
Al'ummar yankin na ci gaba da fama da tabarbarewar tsaro, yayin da masu satar dabbobi da garkuwa da mutane ke ƙara addabar su. Duk da ƙoƙarin da aka yi na samun bayanin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ba mu samu nasara ba wajen jin ta bakin su a kan wannan lamarin.
Katsina Times
[www.katsinatimes.com](http://www.katsinatimes.com)
Jaridar Taskar Labarai