Ziyarar Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Akan Ayyukan Raya Mazabu a jihar Katsina
- Katsina City News
- 07 Aug, 2024
- 245
Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times
A ranar Litinin, 5 ga Agusta, 2024, wata tawaga daga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin mai taimaka wa shugaban kasa akan ayyukan raya mazabu, Hajiya Khadija Omotayo Kareem, ta kai ziyara a garin Katsina domin duba wasu ayyukan da gwamnatin tarayya ta fara a jihar amma aka yi watsi da su.
Hajiya Khadija Omotayo Kareem ta fara ne da duba aikin tashar lantarki ta 132/33KV dake garin Kankia. Masu kula da kwangilar sun bayyana cewa aikin ya kai kashi 95% kuma ana sa ran kammala shi nan ba da jimawa ba. Wannan aikin an fara shi ne tun lokacin marigayi tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar’Adua, amma bai kammala ba har zuwa yanzu.
Bayan haka, tawagar ta ziyarci aikin samar da wutar iska da aka bari a Lambar Rimi wanda ya kwashe sama da shekaru 15 ba tare da an ci gaba da shi ba. A nan, an shirya yin aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana da zai samar da megawatt 10, wanda aka fara a lokacin shugaba Muhammadu Buhari.
A ranar Talata, an shirya taro domin tattaunawa akan ayyukan da gwamnatin tarayya ta fara a jihar amma ba ta kammala ba, wanda aka gudanar a dakin taro na gidan gwamnatin jihar Katsina. Hajiya Khadija ta godewa gwamnatin jihar Katsina akan tarbar da suka yi mata tare da nuna godiyarta ga shugaban kasa akan damar da ya bata domin gudanar da ayyukanta.
Mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Hon. Faruk Lawal Jobe, ya jinjina wa mutanen jihar bisa dattaku da sanin ya kamata, wanda ya hana su shiga zanga-zanga. Ya bukaci Hajiya Khadija da ta kai dukkanin abubuwan da al'umma suka gabatar domin daukar matakin gaggawa daga gwamnatin tarayya.
Daga cikin mahalarta taron akwai Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Katsina, Dakta Faisal Kaita, wanda ya yi tsokaci akan ayyukan da suke bukatar a kammala, ciki har da gina hanyar mota mai hannu biyu daga Kano zuwa Katsina, da hanyar jirgin kasa daga Najeriya zuwa Nijar.
An kuma tattauna batutuwan da suka shafi gina madatsun ruwa, hanyoyin karkara, tsaro, noma da kiwo, cigaban mata da matasa, da kuma maido da shirin ciyar da dalibai da N-Power da shirye-shiryen tallafi.
Hajiya Khadija Omotayo Kareem ta kuma ziyarci makarantar Sakandire ta (GCK) domin ganin wasu ayyukan da aka fara amma ba a kammala ba. Haka kuma ta ziyarci Asibitin koyarwa na (Federal Teaching Hospital Katsina) wanda suma akwai ayyukan da ba a gama ba. Daga nan ta kai ziyara ga mukaddashin gwamnan jihar, Malam Faruk Umar Joɓe, domin nuna godiya da jaddada cewa za a isar da dukkan ayyukan da aka fara ba a kammala ba zuwa ga shugaban kasa.
A karshe, ta ziyarci mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, da Sarkin Daura, Alhaji Dr. Faruk Umar Faruk, tare da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.