Tawagar Gwamnatin Tarayya ta ziyarci Aikin wutar Lambar Rimi a jihar Katsina.
- Katsina City News
- 05 Aug, 2024
- 485
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Wata tawaga da ke karkashin jagorancin Mai tamakama Shugaban Kasa kan Ayyukan Mazabu, Hajiya Khadijat Omotayo Kareem, ta kai ziyara Jihar Katsina don duba ayyukan Gwamnatin Tarayya da aka watsar, Domin sake ginawa.
Da zuwansu, tawagar ta fara da duba aikin tashar wutar lantarki ta 132/33KV da ke Kankia. Masu kula da kwangilar sun bayyana wa Kareem cewa aikin ya kai kashi 95% kuma ana sa ran kammala shi nan ba da jimawa ba. Wannan aiki da aka fara tun lokacin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, ya tsaya cik har zuwa yanzu.
Tawagar ta kuma ziyarci aikin samar da wutar Iska da aka bari a Lambar Rimi, wanda ya kwashe sama da shekaru 15 ba tare da an ci gaba da shi ba. An shirya yin aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana a wannan wurin da zai samar da megawatt 10, wani aiki da aka fara a lokacin Shugaba Muhammadu Buhari.
Haka zalika, tawagar ta duba tashar wutar lantarki da aka bari a Katsina. Mrs. Kareem ta bayyana cewa dalilin ziyarar shi ne don duba wadannan ayyukan Gwamnatin Tarayya don tabbatar da cigaba da su da farfado da wadanda aka watsar.
A jawabin sa, Mai Ba Gwamnan Jihar Katsina Shawara kan Harkokin Wuta, Dr. Hafiz Ibrahim, ya bayyana cewa Gwamnan Katsina ya riga ya aikewa Shugaban Kasa bukatar neman izinin cigaba da aikin wutar Lambar Rimi domin amfanin al’umma.