Hukumar 'Yansandan jihar Katsina Ta Kashe Ɗan Fashin Daji a Kankara
- Katsina City News
- 10 Jul, 2024
- 574
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hukumar 'Yansanda ta jihar Katsina, ta sanar da nasarar da ta samu wajen dakile harin 'yan bindiga a kauyen Gidan Dan Ali da ke yankin Ketare, ƙaramar hukumar Kankara, inda suka kashe ɗan fashin daji ɗaya tare da kwato bindigar AK47 guda ɗaya.
Kakakin rundunar, Sadiq Abubakar, ya bayyana cewa, a ranar Talata, 16 ga Yuli, 2024, misalin ƙarfe 01:05 na safe, bayan samun rahoton hare-haren 'yan bindiga daga hedkwatar 'yansandan ƙaramar hukumar Kankara, DPO na hedkwatar Kankara, CSP Iliyasu Ibrahim, ya jagoranci tawagar 'yansanda, tare da hadin guiwar Katsina State Community Watch Corps (KSCWC) da kungiyar Vigilante, zuwa wurin da lamarin ya faru.
Sun bi sawun 'yan bindigar har zuwa kauyen Bulunkuza da ke yankin Tudun Wada, ƙaramar hukumar Kankara, inda suka yi artabu mai tsanani da su, suka tilasta musu tserewa daga wurin.
Bayan tantance wurin, tawagar ta gano gawar wani ɗan bindiga ɗaya da aka kashe tare da kwato bindigar AK47 guda ɗaya.
Kwamishinan 'yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, yayin yabawa jarumtaka da kwarewar jami'an, ya yi kira ga jama'a da su ci gaba da ba da rahoton duk wani al'amari na aikata laifi ga 'yansanda domin daukar matakin gaggawa.