Gwamnatin Katsina Ta Shiga Yarjejeniya da Kamfanin AFEX Don Bunkasa Noma
- Katsina City News
- 13 Jul, 2024
- 448
A ranar Juma'a, 12 ga watan Yuli, 2024, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD, ya rattaba hannu kan yarjejeniya tare da Kamfanin Samar da Kayan Noma na AFEX. Wannan yarjejeniya na nufin inganta fannin noma a jihar Katsina, tare da samar da kayan aikin zamani da dabarun noma na zamani ga manoma.
A yayin ganawar da aka yi tare da wasu daga cikin shugabannin kamfanin AFEX, shugaban tawagar kamfanin, Mista Ayodeji Balogun, ya bayyana cewa kamfanin nasu zai samar da hanyoyin haɓaka noma da kuma ba manoma jari a jihar Katsina. Daga cikin yarjejeniyar, kamfanin AFEX zai samar da cibiyar sarrafa riɗi a Cibiyar Haɓaka Tattalin Arziki ta Katsina (Katsina State Green Economic Zone), da kuma kafa cibiyar samar da ingantaccen iri a gonar Songhai dake Funtua.
Manoma za su sami kayan aiki da sabbin dabarun noma, tare da hanyoyin da za su ba su damar fitar da kayansu zuwa manyan kasuwanni domin samun riba mai yawa. Wannan zai taimaka wajen bunƙasa fannin noma a jihar Katsina, samar da ayyukan yi, da kuma rage hauhawar farashin kayan abinci.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana gamsuwarsa da wannan yarjejeniya, yana mai cewa AFEX kamfani ne mai tarihi da kwarewa wajen kawo cigaba a fannin noma. Ya ƙara da cewa, farfado da martabar noma yana daga cikin manufofin gwamnatinsa, kuma wannan yarjejeniya zata taimaka wajen cimma wannan buri.
A ƙarshe, Gwamnan yayi kira ga sauran kamfanoni masu zuba jari, daga cikin gida da waje, su zo jihar Katsina don taimaka wajen farfado da fannin noma da kasuwanci a jihar.
Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnati, Hon. Jabiru Salisu Abdullahi, Sakataren Gwamnan, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, Daraktan Hukumar Bunƙasa Jari ta jihar Katsina, Alh. Ibrahim Tukur Jikamshi, da Mai ba Gwamnan Shawara kan Tattalin Arziki, Khalil Nur Khalil, na daga cikin wadanda suka halarci zaman.