'Yan Sanda Sun Dakile Yunƙurin Sace Mutane a Katsina, Sun Kashe 'Yan Bindiga Uku
- Katsina City News
- 08 Jun, 2024
- 525
Maryama Jamilu Gambo Saulawa, Katsina Times
A ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan 'Yan Sandan Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, rundunar 'yan sanda ta samu nasarar dakile yunƙurin sace mutane, tare da ceto duk wadanda aka yi garkuwa da su, kuma ta kashe 'yan bindiga uku.
A ranar 7 ga Yuni, 2024, an samu rahoto a hedkwatar 'yan sanda ta karamar hukumar Sabuwa cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kauyen Duya, Maibakko ward, karamar hukumar Sabuwa, inda suka yi garkuwa da mata da dama.
Bayan samun rahoton, shugaban 'yan sandan sashen Sabuwa, CSP Aliyu Mustapha, tare da haɗin gwiwar 'yan sa-kai, suka tattara tawagar jami'an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru. Da 'yan bindigar suka ga zuwan jami'an tsaro, sai suka fara harbi, wanda tawagar jami'an tsaron ta maida martani, inda ta samu nasarar dakile yunƙurin satar mutanen tare da ceton duk waɗanda aka yi garkuwa da su.
Bayan an kammala duba wurin da abin ya faru, an samu gawarwakin 'yan bindiga uku da aka kashe.
Kwamishinan 'Yan Sandan, yayin da yake yabawa jami'an tsaron bisa kwarewarsu da jarumtarsu, ya sake jaddada kudurin rundunar na tabbatar da tsaron lafiyar al'umma da dukiyoyinsu a jihar.