TSARO A ZAMFARA: JADAWALIN IRIN ƘOƘARIN DA GWAMNA DAUDA LAWAL YA YI CIKIN SHEKARA ƊAYA
- Katsina City News
- 30 May, 2024
- 530
Mayu 29, 2023
A wannan rana ne aka rantsar da Dauda Lawal a matsayin Gwamnan Jihar Zamfara
Yuni 1, 2023
A wannan rana, Gwamna Dauda Lawal a matsayin sabon gwamna, ya amshi rahoton halin da ake ciki daga shugabannin ɓangarorin tsaro na Jihar Zamfara.
Yuni 1, 2023
A wannan rana, Gwamna Dauda Lawal ya tattauna da AIG me wakiltan shiyya ta 10, Bello Sani Dalijan, da kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda na Zamfara (a lokacin) CP Mohammed Bunu a ofishinsa da ke gidan gwamnati. Sun tattauna matsalar tsaro da abin da ya kamata a yi.
Yuni 12, 2023
A wannan rana ne, Gwamna Dauda Lawal ya tattauna da Kwamandan Sojoji na shiyya ta takwas, General GM Mutkut, inda suka tattauna sabon salon da rundunar sojoji za su ɗauka wurin yaƙi da ‘yan bindiga.
Yuni 14, 2023
A wannan rana ne Gwamna Dauda Lawal ya tafi babban birnin tarayya, Abuja, inda ya tattauna da Shugaban Rundunar Sojoji, Janar Lucky Irabor a hedikwatar tsaro ta Abuja. Gwamnan ya roƙi a aika da ƙarin sojoji zuwa Zamfara.
Yuni 21, 2023
A wannan rana ne, Gwamna Dauda Lawal ya amshi baƙuncin Group Captain Sekegor a ofishinsa, inda suka tattauna hanyoyin da sojoji za su inganta tsarin sa ido ta hanyar amfani da na’urori da kuma yadda za a ƙaddamar da hare-hare kan ‘yan bindiga.
Yuli 12, 2023
Bayan an naɗa sabon Shugaban Rundunar Sojoji, Janar Chris Musa, Gwamna Dauda Lawal ya sake komawa Hedikwatar Tsaro, inda ya yi mishi bayanin yanayin tsaron da ake ciki a Zamfara. Tare da neman tallafin rundunar sojojin kan hanyoyin da za a bi a yi yaƙi da ‘yan bindiga.
Yuli 24, 2023
A wannan rana ne Gwamna Lawal ya yi tattaunawar sirri kan matsalar tsaro da mabambantan masu ruwa da tsai a babban birnin tarayya Abuja. Waɗanda suka haɗa da NSA, Mallam Nuhu Ribadu, Shugaban Rundunar Tsaro, Chris Musa, da kuma shugaban rundunar sojojin ƙasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja.
Agusta 14, 2023
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya amshi baƙuncin Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja da sauran sojoji daga runduna ta takwas. Sun ziyarci gwamnan ne a wata ziyarar aiki, da kuma bibiyar irin abin da rundunar sojin ke yi a dazuka.
Agusta 17, 2023
A wannan rana, Gwamna Dauda Lawal tare da Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago sun ziyarci NSA, Mallam Nuhu Ribadu a Abuja. Inda suka tattauna batun faɗaɗa faɗa da ‘yan bindiga.
Agusta 18, 2023
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci Babban Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya, Kayode Adeolu Egbetokun don tattauna yadda za a ƙarfafi ‘yan sanda wurin yaƙar ‘yan bindiga. Haka nan kuma a wannan rana, Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci Kwanturola Janar na NSCDC, Ahmed Abubakar Audi a hedikwatar NSCDC da ke Abuja.
Oktoba 12, 2023
A wannan rana ne Gwamna Lawal ya amshi baƙuncin Kwamandan NAEC, Majo Janar Bello Alhaji Tsoho a ofishinsa da ke Gusau. Ziyarar da ta taimaka wurin inganta makarantun soji da ake da su a Zamfara.
Nuwamba 9, 2023
A wannan rana, Gwamna Lawal ya jagoranci Taron Majalisar Tsaro ta Jihar Zamfara, inda aka fitar da sabbin tsare-tsare na yaƙar ‘yan bindiga.
Nuwamba 30, 2023
A wannan rana ne Gwamna Lawal ya ziyarci wurin da ake horas da Rundunar Askarawan Zamfara. Waɗanda gwamnatinshi ta samar don magance matsalar tsaron jihar Zamfara.
Disamba 26, 2023
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya zanta da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin tattauna matsalar tsaron da ke damun Jihar Zamfara.
Janairu 18, 2024
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya haramtawa sarakuna bayar da takardar izinin haƙar ma’adinai. Matakin da ya daƙile yawaitar ayyukan ‘yan bindiga.
Janiru 28, 2024
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya halarci taro kan matsalar tsaron Arewa Maso Yamma wanda gamayyar ƙungiyoyin arewa ta shirya a Abuja. A wurin taron ya gabatar da jawabi kan irin ƙalubalen da Zamfara ke fuskanta.
Janairu 31, 2024
A wannan rana ne Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da Askarawan Zamfara. Waɗanda tuni sun fara aiki don taimakawa jami’an tsaro a yaƙi da ‘yan bindiga.
Fabrairu 7, 2024
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da kwamitin mutum 21 na Cibiyar Samar da kuɗaɗen tsaro ta jiha. Kuɗaɗen da za a yi amfani da su wurin yaƙar matsalar tsaro.
Maris 9, 2024
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci ƙaddamar da ofishin Cibiyar Samar da kuɗaɗen tsaro ta Jihar Zamfara.
Maris 13, 2024
A wannan rana ne Gwamna Lawal ya rattaba hannu kan dokar da ke haramta amfani yin amfani gilashi me duhu, sayar da biredi ba tare da shaidar kamfani a jiki ba. Duk an yi wannan ne don a daƙile kai kayan abinci ga ‘yan bindiga.
Maris 26, 2024
A wannan rana, Gwamna Dauda Lawal ya tattauna da Shugaban Rundunar Tsaro, Janar Chris Musa a hedikwatar tsaro ta Abuja, inda ya nemi a aika da ƙarin sojoji Zamfara.
Afrilu 22, 2024
A wannan rana ne Gwamna Dauda Lawal ya tattauna da mataimakiyar Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, Mrs Amina Mohammed a New York, inda ya bayyana cewa ana buƙatar fasahar zamani wurin yaƙi da ‘yan bindiga.
Mayu 2, 2024
A wannan rana gwamna Dauda Lawal ya amshi baƙuncin mahalarta kwas na Cibiyar Tsaro (NISS), wanda suke bahasi kan hanyoyin amfani da kimiyyar zamani wurin yaƙi da rashin tsaro.
Mayu 3, 2024
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya bayyana fara biyan tsofaffin ma'aikatan jihar bashin haƙƙoƙin su na barin aiki, wato Garatuti, wanda suka biyo tun na shekarar 2011, kuɗaɗen da suka haura Naira Biliyan Huɗu.
Mayu 10, 2024
A wannan rana ce Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ƙoƙarin sojoji game da yaƙin da su ke yi a kan 'yan bindigar da suka addabin jihar, inda ya ce ƙwalliya na biyan kuɗin sabulu, jami'an tsaron na samun nasara kan 'yan bindigar. Ya kuma yaba da ƙarin sojojin da turo zuwa Zamfara don ƙara fatattakar 'yan ta'addan.
Mayu 15,2024
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon tan 42,000 na kayan abinci daban-daban ga marasa galihu a Zamfara, inda ya wannan rabon kayan abinci y zo daidai lokacin da jama'a ke buƙatar sa.
Mayu 22, 2024
A wannan rana ce Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar wa da shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta jihar, cewa gwamnatin sa za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira Dubu Talatin a wata mai zuwa na Yuni.
Mayu 23,2024
A wannan rana Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci zaman majalisar tsaro ta jihar, inda ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na bayar da ƙarin tallafi ga dakarun da ke yaƙi da ’yan bindiga a Zamfara.
Mayu 25,2024
A wannan rana Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana ilimi a matsayin wani tsani, na kaiwa ga samun duk wani abin nema a duniyar nan. Ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar wajen bikin yaye ɗaliban Jami'ar tarayya da ke Gusau.