Tinubu ya jaddada Aniyarsa ta kawo karshen 'Yanbindiga a Zamfara
- Katsina City News
- 13 Apr, 2024
- 650
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin sa na kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga da ta addabi Jihar Zamfara.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin tura ƙarin sojoji tare da ci gaba da kai farmaki kan ’yan ta'adda a Zamfara.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce, shugaba Tinubu ya karɓi baƙuncin wasu gwamnonin jihohi da shugabannin majalisar dokokin ƙasar a gidansa da ke Legas.
A cewar sanarwar, tawagar wacce ke ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ta kai wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu gaisuwar Sallah a ranar Juma’a.
“A yayin tattaunawa da Gwamna Dauda Lawal, shugaba Tinubu ya tambaye shi game da matsalar tsaro a Jihar Zamfara.
“Gwamna Lawal ya bayyana wa Shugaban irin ci gaba da kuma yaƙin da sojoji ke yi kan 'yan bindiga a jihar.
“Daga nan sai Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Gwamnan irin aniyar sa ta ganin ƙarshen ayyukan 'yan bindiga a jihar, inda ya ƙara da cewa ya bayar da umurni ga sojoji da su ɗauki tsauraran matakai a kan 'yan ta'addan, ya kuma tura ƙarin wasu sojojin zuwa jihar."
"Shugaban ya kuma buƙaci Gwamna Lawal ya rinƙa sanar da shi a kai, a kai halin da tsaro ke ciki a jihar, don a samu haɗin hannu wajen yaƙi da 'yan bindigar."