Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ayyana ilimi a matsayin wani ginshiƙi mafi muhimmanci ga ci gaban jihar Zamfara.
- Katsina City News
- 20 Mar, 2024
- 533
A Larabar nan ne ɗaliban makarantar 'Leadsprings International Schools' suka karrama Gwamna Lawal a gidan gwamnati da ke Gusau.
Kamar yadda ya ke ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau yau, ya bayyana cewa waɗannan yara su kuma miƙa wa Gwamnan wasu buƙatu guda bakwai masu muhimmanci, waɗanda su ke sa ran cimma a nan gaba.
Malam Idirs Bala ya ce, waɗannan tsammani da ake son cimma a aƙibar Zamfara, sun haɗa da babban birnin jihar, Gusau; sashen kiwon lafiya; harkar jiragen sama na Zamfara; fasaha; noma da sashen tattalin arziki, masana'antu da kamfanoni.
Cikin jawabin da ya yi wa waɗannan yara, Gwamna Dauda ya ƙara jaddada aniyar sa ta yin garambawul a harkar ilimi a jihar.
Gwamnan ya ce, “Ilimi ne abu na ɗaya cikin muhimman abubuwan da gwamnati na ta sanya a gaba, na biyu kuma, shi ne harkar tsaro. Sai dai harkar ilimin mu ba ta tafiya yadda ya kamata a lokutan baya. A kowane lokaci jihar Zamfara tana zamowa ta ƙarshe a harkar ilimi, wannan ne ya sa na sanya dokar ta-ɓaci a harkar ilimin.
“Matakan sun haɗa da ɗaukar ƙwararrun Malaman da suka cancanta, samar da gine-gine da isassun kayan aiki, tare kuma da samar da hanyoyin koyarwa irin na zamani.
“Gwamnati na ba za ta gajiya ba, wajen sake fasalin harkar ilimi, ta yadda zai biya buƙatun al'ummar mu.
Daga nan kuma sai Gwamnan ya nuna jin daɗin sa bisa irin misalin ingantaccen ilimin da yaran suka nuna masa sun samu a makaranar tasu. Ya kuma gode wa Hukumar wannan makaranta ta 'Leadsprings International School' bisa wannan karramawa da suka yi masa.
“Na ji daɗi da ganin irin yanayin karatun ku da kuka nuna mana, wannan ya na nuni da cewa ɗaliban makarantar 'Leadsprings International School' a shirye su ke su goga kafaɗa da kowa a faɗin duniyar nan.
“Ina godiya da wannan karramawa. Gwamnati na za ta ƙarfafa maku a duk inda za ta iya. Ina kira ga sauran makarantu masu zaman kansu su kwaikwayi wannan kyakkyawan aiki na ku.
Cikin nasa jawabin sa, mai makarantar 'Leadsprings International School, Danjuma Sule ya bayyana cewa makarantar sa a shirye ta ke ta tafi da tsarin ilimin gwamnatin jihar Zamfara.
“Muna jinjina ga gwamnatin ka bisa irin jajircewarta wajen samar da yanayin karatu mai kyau a duk faɗin jihar. Muna kuma godiya da aniyar ka ta ɗaukaka ilimin mata a jihar. Yanzu haka, makarantar 'Leadsprings International Schools' muna da ɗalibai mata 386 a ajujuwa daban-daban, kuma muna nan muna nuna masu hanyoyin da za su zama masu amfani ga ci gaban Zamfara.