ƳAN BINDIGA SUN KAI HARI KANDAWA TA BATSARI
- Katsina City News
- 08 Feb, 2024
- 646
Misbahu Ahmad @ Katsina Times
Ƴan bindiga sun kai hari garin Kandawa ta ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Lamarin ya faru a daren ranar laraba 07-02-2024.
Tun da yammacin ranar aka ga ayarin ɓarayin kan babura kimanin hamsin sun fito daga daji, sun tunkari ƙauyukan dake yankin arewa maso gabbacin Batsari. Wani basarake ya bayyana mana cewa "mun shaida ma masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, ɓarayi sun fito amma dai ba'a ɗauki mataki ba har suka kai wannan hari"
Wani mazaunin garin ya bayyana ma jaridun Katsina Times, yadda abun ya faru, inda yace ɓarayin sun afka masu cikin shirin yaƙi, suna harba manyan bindigu kamar za su ƙarar da garin. Sun kashe wata tsohuwa, kuma sun ƙona motar ƴansandar kwantar da tarzoma dake aikin bada tsaro a garin.
Sannan sun yi garkuwa da mutane 20 akasarin su mata ne. kuma sun kwashi dabbobi masu yawa.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762