Yadda Baturen Ƴansanda DPO Yaƙi Karɓar Cin Hanci Na Naira Milyan Ɗaya Ya Kama Ɗan Ta'addar Daji...
- Katsina City News
- 28 Jan, 2024
- 544
Rundunar ƴan sandan Najeriya tayi nasarar tarwatsa wata maboyar ƴan ta'addar daji tare da kama gawurtaccen Ɗan ta'addar daji da ya kashe wata Yarinya mai suna Nabeeha wadda aka kashe a Bwari babban barnin tarayyar Najeriya.
Sufeton ƴan sandan Najeriya ya yabama Ɗan sandan da yaƙi karɓar kuɗin cin hanci da rashawa a wurin wani Ƙasurgumin Ɗan Bindiga a garin Tafa jihar Kaduna dake kan iyakar jihar Neja da Birnin Tarayya.
Rundunar ƴan sandan, a ranar 20th January 2024, tayi nasarar kama wani Bello Mohammed, Ɗan kimanin Shekaru 28, Ɗan asalin jihar Zamfara a jihar Kaduna.
Baturen ƴan sanda dake kula da shiyyar Tafa bayan samun bayanan sirri ya kai sameme wata Otel a garin na Tafa, Inda yayi nasarar kama Bello, da tsabar kuɗi Naira Milyan Biyu da Naira Dubu Ɗari Biyu da Hamsin #2.25m, Wanda ake kuɗin fansa ne da ya karɓa.
Da ake tuhumar shi ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin waɗanda suka sace Iyalin, Barrister Ariyo a Bwari, FCT, a ranar 2nd January 2024, Inda suka kashe wasu daga cikin waɗanda suka sace hadda Yarinyar nan mai suna Nabeeha, a ranar 13th January, 2024, a maboyar su dake jihar Kaduna.
Bello yayi ƙoƙarin baiwa DPO cin hanci yayin da yazo kama shi na tsabar kuɗi Naira Milyan Ɗaya amma DPO yaƙi amincewa tare da aiwatar da aikin shi.
Babban Sufeton ƴansanda Kayode Adeolu Egbetokun, Ph.D., NPM, ya bada Umarnin a miƙa shi ga rundunar Jami'an tsaro ta musamman wato DFI-IRT domin ci gaba da bincike akan lamarin, Bello dai ya amsa cewa yana tare da dabar wani Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Mai Gemu wanda akafi sani da Godara da Yana cikin wasu ƴan ta'addar da sukayi arangama da Jami'an tsaro amma basu sha da daɗi ba.
Kayode ya yabama DPO na Tafa, SP Idris Ibrahim, akan yadda ya gudanar da aikin shi bisa ƙwarewa da amana ya kuma tabbatar ma da ƴan Najeriya cewa ba zasuyi ƙasa a guiwa ba wajen Zaƙulo duk wasu ƴan ta'adda a faɗin ƙasar nan.