ƁARAYIN DAJI CIKIN KAYAN SOJOJI SUN SACE MUTANE TALATIN JIHAR KATSINA
- Katsina City News
- 22 Jan, 2024
- 620
Daga Misbahu Ahmad @Katsina Times
Ɓarayin daji masu garkuwa da mutane sun sace mutane talatin a ƙauyen Tashar nagulle dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Ɓarayin sun afka ma mutanen ƙauyen da misalin ƙarfe 08:00pm na daren ranar lahadi 21-01-2024. Shigar su ƙauyen keda wuya sai suka harba bindiga sau biyu, sannan suka riƙa bin mutane da gudu suna kamawa, suna cewa ku dakata mu maaikata ne, mun zo mu taimake ku amma kuna ta gudu to duk wanda ya gudu za mu harbe shi. wasu kuma suka shiga gidaje suka zaƙulo mutane. Wannan dalilin yasa suka samu damar tattara mutane da yawa, saboda ɓarayin sun yi shigar sojoji ta yadda duk wanda ya gansu zai amince maaikata ne.
Wani da ya ƙubuto daga hannun ɓarayin ya bayyana mana cewa lokacin da ɓarayin suka isa da su wajen baburan su sai suka ƙirga su, su talatin da ɗaya maza da mata ciki hadda ƴan mata da matan aure, sannan suka ce kowa ya hau babur, ana cikin ruguguwar hawan babura ya samu mafita ya ƙubuce masu ya dawo gida.
Mutanen garin sun tabbatar mana da faruwar lamarin.amma hukumomin yan sanda sun ce suna binciken abin da ya faru.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762