YA AKA KASHE KWAMANDAN JAMI IN TSARON AL UMMA NA KIRTAWA SAFANA?
- Katsina City News
- 31 Dec, 2023
- 558
Muazu Hassan @Katsina Times
Kwanakin baya Barayi sukayi kwantan Bauna suka kashe jarumin kwamandan nan na jami in tsaron al umma na yankin kirtawa Tanimu sada wagili.dake karamar hukumar safana, jahar Katsina.
Tanimu yana da mutane talatin karkashin sa kuma ya hana barayi sakat, suna tsoron shi kamar yunwar cikinsu.
Kashe kwamandan ya girgiza al ummar karamar hukumar safana, musamman yankin kirtawa inda aka San irin gudummuwar da yake bayarwa wajen kare yankin daga hare haren miyagun barayin daji masu dauke da Muggan makamai.
Kashe kwamandan Wanda aka fi sani da Tanimu wagili ya sanya gwamnatin Katsina ta aika da tawaga mai karfi don jaje da ta aziyya ga iyalan shi da kuma al ummar kirtawa ,gwamnatin ta kuma aika da tallafin kudi ga iyalan shi.
YA AKA KASHE SHI?
Kisan nashi yazo da zarge zarge musamman akan wani shugaban mulki a karamar hukumar ta safana, Wanda aka ce sakacin sa da wani sa baki da yayi na a saki Wanda ake zargin cikin daren,ya jawo aka yi ma Tanimu kwantar bauna aka kashe shi.
Labarin da jaridun Katsina Times ta samu daga majiyoyi daban daban sune, jami an tsaron al umma na yankin safana sun kamo wani mai suna Dan jamilu mutumin salihawal kalgo an kamo shi a garin Wagini dake karamar hukumar batsari, Wanda ake zargi yana hudda da barayin daji.
Wasu sun fada ma jaridun mu cewa dan jamilu yaro siyasa ne ga shugaban karamar hukumar safana kabir Umar,wasu kuma sunce baida alakar siyasa dashi, amma garinsu daya kawai.
Bayan kama Dan jamilu,jami an tsaron na al umma ,sun tuhume shi wani da ya samu labarin yadda akayi binciken ya tabbatar ma da jaridun mu cewa ,Dan jamilu ya tabbatar masu da cewa bisa tilas da tsoro ya sanya yake, mu amalar kasuwanci da fulanin daji cikin su, wasu barayi ne.mai bamu labari yace Dan jamilu yace amma shi bai taba zama infoma na barayin ba. Yace kasuwancin da yake dasu, na tilas ne suke sayen kaya wajen sa.
Wata majiyar tace, ana tsakar binciken. Yana bayanin dangantakar su,sai aka fara buga jami an tsaron na al umma waya cewa su saki Dan jamilu.saboda yana da ciwon hawan jini.kuma bai da wata alaka da barayi.
Majiyar mu tace kwamandan safana yace a bari sai da safe a sake shi domin dare yayi, an ce wai amma aka matsa ma kwamandan da waya ya sake shi.ance wai wayar har daga wani shugaban mulki a karamar hukumar safana.
Aka ce a dauki Dan jamilu a kai shi garin kukar samu a damka shi ga wani mai suna murtala social.
Majiyar mu tace, matsin lamba da waya ta sanya cikin daren aka ce Tanimu wagili ya dauki Dan jamilu ya kaishi kukar samu ya damka ma murtala social.
Akan hanyar ta baro garin barayi suka kwanta masa dajin dake tsakanin kukar samu zuwa kirtawa, suka kayar dashi bisa babur suka yi harbe shi da bindiga taki kamawa sai suka samu wayar kebur da ita suka tsinka wuyan shi.
TAMBAYOYI....
A lokacin da mukaji raayoyin mutanen tambayarsu.su wa suka matsama kwamandan safana da waya akan cewa lallai sai ya saki Dan jamilu a cikin daren nan? An samo muryar wayoyin da aka rika yi ma kwamandan ? Me masu wayar ke fadi na sakin Dan jamilu?
Ina Dan jamilu? Yana yawon shi ko anci gaba da binciken shi.?
Majiyar mu ta tabbatar mana an jami an tsaron al umma sun kama murtala social kuma yana hannun su..
KIRAYE KIRAYEN AL UMMA.
Kashi dari bisa dari na wadanda muka zanta dasu bukatar su itace, gwamnatin Katsina ta kafa Kwamitin bincike mai zaman kansa Wanda ya kumshi yan sanda da jami an tsaron DSS su binciki ya akayi Tanimu wagili ya fada tarkon kwantar bauna har aka kashe shi?
Jaridun mu sunyi magana da shugaban karamar hukumar ta safana inda yace shi bai da abin da zai ce amma ana iya tuntubar kwamandan safana na jami an tsaron al umma.
Munyi kokarin magana da kwamandan na safana,amma duk lambobinsa da aka bamu babu mai tafiya.mun kuma aika masa da sakon waya ba amsa.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 080 57777762