KWAMANDOJIN YAKIN GAZZAH (5).
- Katsina City News
- 11 Dec, 2023
- 657
MUHAMMAD DHAIF (محمد ضيف)- HAFSAN HAFSOSHIN RUNDUNONIN KASSAM (1).
Muhammad Dhaif shine hafsan hafsoshin Kataa'ibu Kassam, (Qassam Brigades), ko kuma Rundunonin Kassam da Hausa, watau bangaren mayakan kenan na kungiyar Hamas, kuma shine wanda lokacin da Hamas ta kai wa Isra'ila hari a ranar 7/10/23 ya yiwa duniya jawabin dalilan kai wannan hari.
A tsarin gudanarwa na Hamas wannan bangare na mayakan yana cin gashin kanshi ne, ba kai tsaye karkashin sashen siyasa ya ke ba. Ma'ana wannan sashe na mayaka yana da damar shirya wasu hare-hare a kan yahudawa ba sai ya nemi amincewar sashen siyasa ba.
An saka wa wannan sashe suna ne daga sunan wani shehin malami mujahidi dan kasar Suriya mai suna Sh. Izzuddin Al-kassam. Wannan malami ya zauna ne a kasar Falasdin, kuma shine ya fara jagorantar jihadi da makamai a kan turawan Biritaniya da ke mulkin mallaka a Falasdin.
Turawan Biritaniya sun fara mulkin mallaka a Falasdin ne a shekarar 1917. Ya zuwa shekarar 1925 makircinsu na mika kasar ga yahudawa ya bayyana kiri-kiri ta yadda suka bude wa yahudawan kofar tarewa da yin zaman dirshan a kasar, har a wannan shekarar suka bude Jami'ar koyon harshen Ibraniyanci (Hebrew), wanda shine harshen yahudawa a birnin Kudus.
Saboda dukkan matakan siyasa da diflomasiyya da irin su Muftin Falasdin na wancan lokaci, Sh. Alhaj Amin Alhusainy suka yi ta dauka domin dakatar da turawan Biritaniya daga shirin nasu na mika Falasdin ga yahudawa ya ci tura sai shi Sh.Izzuddin Al-kassam ya fara hada kungiyar jihadi da makamai a shekarar 1932, domin yakar turawan Biritaniya da kuma kungiyoyin ta'addanci da yahudawa suka samar a cikin kasar tare da yarjewar turawan.
Sh. Kassam ya jagoranci karawarshi ta farko da turawa a shekarar 1935 ya kuma samu shahada. Amma tun daga lokacin dukkan mukawamar da Falasdinawa suka yi da turawa ko yahudawa da sunan jihadi suna daukar ta a matsayin ci gaba da aikin da Kassam ya fara, don haka sukan kiranta da "harakatu Izzuddin Al-kassam", ko kuma "harakatul Kassamiyyah".
Da haka ne suma Hamas suka kira rundunoninsu na jihadi da sunan "Kataa'ibu Kassam".
A wannan karo zamu duba tarihin wanda ya ke shine a halin yanzu hafsan hafsoshin wadannan rundunoni, watau Muhammad Dhaif in sha Allah.
Malam Aminu Aliyu Gusau
Modibbon Gusau.
8/12/23.
Mun ciro daga shafin Attajid media dake Facebook