Uwargidan Gwamnan jihar Katsina ta bude shirin horas da Malaman Makaranta da Dalibai na kwanaki uku.
- Katsina City News
- 23 Nov, 2023
- 797
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A kokarinta na ciyar da ilimi gaba, uwargidan gwamnan jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Radda, ta jaddada kudirinta na hada gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu, cibiyoyin ilimi, da masu ruwa da tsaki, don habaka Ilimin jihar Katsina. Zulaihat ta jaddada wannan kiran ne a yayin buɗe taron horo na kwanaki uku a gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis, 23 ga Nuwamba, 2023.
Horaswar wadda kungiyar "Safe Space Humanitarian Initiative" (SASHI) ta shirya tare da hadin gwiwar shirin AGILE da ma'aikatar ilimi ta jihar, ya mayar da hankali ne kan hanyoyin gaggawa da matakan kare kai ga malamai da dalibai.
Hajiya Zulaihat Dikko ta jaddada muhimmiyar rawar da irin wadannan tsare-tsare ke takawa wajen samar da ingantacciyar muhallin koyo a fadin makarantun jihar Katsina.
Da yake karin haske kan tasirin shirin, Dokta Mustapha Shehu, shugaban shirin AGILE a jihar Katsina, ya bayyana cewa shirin horaswar ya riga ya dauki dalibai dubu biyar. Kuma ana saran horas da Dalibai Maza dubu goma sha bakwai da Dalibai Mata dubu goma sha tara nan da shakarar 2025
A jawabinta ga mahalarta taron, kwamishiniyar Ilimin firamare da sakandire Hajiya Hadiza Abubakar Yar’adua ta bayyana cikakkiyar manufar gwamnatin jihar na farfado da ilimi a fadin jihar baki daya.
Da take jaddada wajibcin samun ci gaba mai dorewa daga masu ruwa da tsaki, Hajiya Zulaihat Dikko ta bukaci a ci gaba da marawa ayyukan gwamnati baya. Ta bayyana irin tasirin da shirin na SASHI da AGILE ke da shi, wanda bai tsaya a kan Ilimi kadai ba ya hada da lafiya, sauyin yanayi, da bangarori daban-daban na ci gaban al'umma.
Manyan mutanen da suka bayar da gudumawa wajen gabatar da jawabai sun hada da Dokta Kabir Magaji, shugaban hukumar kula da Ilimin bai daya ta jihar Katsina "SUBEB," Alh. Sada Ibrahim Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Malamai (TSB), da Dokta Halima Yalwa Adamu da sauransu.
Taron wanda ya samu halartar Hajiya Asma'u Faruk Lawal Jobe, uwargidan mataimakin gwamnan jihar Katsina, da wasu manyan sakatarorin dindindin na jihar Katsina, da wasu manyan mutane irin su Hajiya Binta Hussaini Dangani shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina, ya nuna irin sadaukarwar da aka yi na hadin gwiwa. domin bunkasa ilimi da walwalar al'umma a jihar Katsina.