Dambarwa da rikicin shugabanci da kungiyar Katsina United a Katsina United, a ina matsalar take?
- Katsina City News
- 23 Nov, 2023
- 499
- Alhaji Umar Isyaku Ogunse
A matsayi na na tsohon Ciyaman na Talba Strikers Football, tsohon Ciyaman na Sports Writers, Katsina State, kuma mai ruwa da tsaki a harkokin wasanni a jihar Katsina, ni Alhaji Umar Isyaku Ogunse ina kira ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya gaggauta yin bincike a kan rikicin dake a kungiyar kwallon kafa ta Katsina United domin dawo da martabar ta.
Gaskiya mai girma Gwamna akwai matsala sosai a kungiyar wadda za ta iya jawo ma kungiyar nakasu da ci baya a harkokin wasanni a jihar.
Misali, yanzu haka kungiyar ta Katsina United tana a mataki na 11 a teburin gasar firimiya bayan ta buga wasannin ta na wannan kakar wanda hakan ya samu asali ne saboda kungiyar ta tafka rashin nasara a wasannin da ta je waje ta buga kuma a gidan ta ma tana buga canjaras ko kunnen doki inda ake raba maki.
Haka zalika dakatarwar da aka yi wa mai horar da yan wasan kungiyar (Technical Adviser) ya kara jefa kungiyar cikin matsalar da ta dade bata fada ba.
Wadannan matsalolin idan suka cigaba, za su iya jefa kungiyar a gurbin gajiyayyu kamar yadda ya faru a baya domin wasu daga cikin shugabannin dake gudanar da kungiyar ba kwallon ce a gaban su ba.
Tabbas korar mai horar da kungiyar da aka yi zai jawo wa jihar asara ta miliyoyin kudade domin kwantaragin sa bata kare ba kuma dole sai an biya shi ragowar kudaden sa na albashi da suka rage.
Daga karshe ina kira ga Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya sa a bincika masa ra’ayoyin al’umma dangane da halin da kungiyar take ciki domin samun hanyar lalubo bakin zaren.