RIKICIN PDP A KATSINA: LAMARIN SAI KARA MUNI YAKE ...Safana tayi korafin kar a chanza mata sunaye.
- Katsina City News
- 21 Nov, 2023
- 1118
Muazu Hassan @Katsina Times
Yayin da gwamnatin Katsina karkashin jagoranci jam iyyar APC ke ta shimfida ayyukan cigaba kamar yadda suka tsara kuma suke ta nade naden mukaman gudanar da mulki.
Jam iyyar adawa ta PDP kullum sai tsunduma take bisa sabon rikici da rarrabuwar kai.wasu "yan jam iyyar na zargin wani na son kwace ta da sanya ta cikin aljihun sa.wanda ake zargin yana da kudin da zai iya haka, suna zargin yana son rike jam iyyar har zaben 2027 don yayi takara a cikin ta.
Ko a karshen satin da ya gabata, masu ruwa da tsaki na jam iyyar sunyi taro a Kaduna, taron da aka zargi wani yaje da wadanda basu cancanta shiga taron ba da niyyar in an so ayi abin da bai masa dai dai ba ya tada rikici a taron.
"Mun samu labarin take taken shi, sai muka ki tattauna duk abin da zai kawo fitina, muka biyo masa ta wata hanyar haka aka tashi taron lafiya" inji wani da ya halarci taron.
Nadin da akayi na shugabannin riko nakananan hukumomi na cikin abin dake tafasa jam iyyar, kananan hukumomi daya bayan daya sai kin amincewa suke da wadanda aka shelanta, za a nada masu ko kuma an nada masu.
Karamar hukumar safana itace ta baya bayan nan da masu ruwa da tsaki nasu suka rubuta ma Kwamitin shugabannin riko na jaha Cewar basu amince da duk wani chanji suna da za ayi na yan Kwamitin da suka amince daga karamar hukumar ba.
Kamar yadda wasikar da Katsina Times ta gani, masu ruwa da tsaki na jam iyyar PDP daga karamar hukumar safana na zargin an chanza sunayen da suka sani sun bada.don haka suka rubuta takardar korafin cewa duk wani yunkurin chanza suna ko daya basu yadda dashi ba kuma ba zasu amince ba.
Jam iyyar ta PDP ta samu koma baya sosai a Katsina ta rasa wasu yan majalisar tarayya biyu Wanda kotun daukaka kara ta amsa ta baiwa APC.
Wata rigimar dake gaban jam iyyar itace wata Shari a dake kotu , Wanda wasu shugabannin jam iyar a baya suka kai kara.
Da yawa yan jam iyyar na ganin matsalar ta guda daya ce kuma sai an hadu da murya daya anyi maganin matsalar .Matsalar itace wani yana son ko ta halin kaka sai yayi takara cikin ta a shekarar 2027.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762