An kaddamar da tsige shinkafa a gonar dadin Kowa dake karamar hukumar funtua

top-news

Kamar ko wace shekara, a wannan karon ma Gimbiya 'yar sarkin noman Funtua, Garba Dan Ammani ta kaddamar da bikin tsige shinkafa a gonar na ta wacce aka fi sani da "Dadin Kowa Farm" da ke karamar hukumar Funtua a garin Dakamawa.

A yayin bikin tsige shinkafar, Gimbiyar ta yi jawabi a inda ta fara da cewa: " Da farko dai ina mika godiya ta musamman ga Allah madaukakin sarki da ya kawo mu wannan lokacin, hakika daminar bana tayi albarka domin ko mun ga amfanin gona kwarai da gaske, munyi shukokinmu lafiya gashi Kuma zamu fara girbe abinda muka shuka"


"Hakika daminar bana ta yi albarka ba kuma abinda za mu ce sai Alhamdulillahi, domin kuwa mun shuka amfanin gona kala daban-daban tun daga Masara, Farin Wake, Waken Suya, Gero, Dawa da dai sauransu wanda yanzu haka mun taru a nan ne domin kaddamar da tsige daya daga cikin amfanin wannan gona ta Dadin Kowa wato shinkafa".

A karshe Gimbiyar ta kara da godewa jami'an tsaro na rawar gani da su ka taka wajen basu tsaro a yayin gudanar da noman bana tun farkon damina har izuwa yau da ake gudanar da tsige daya daga cikin amfanin wannan gona.