Zambo cikin aminci: Waƙoƙin Rarara a siyasar Kano
- Katsina City News
- 29 Oct, 2023
- 1313
Daga FARFESA ABDALLA UBA ADAMU
Fassara: HASSAN AUWALU MUHAMMAD
A cikin shekaru 43 da suka gabata da na kasance mai bincike, akwai ɓangarori biyu da na ƙi karkatar da aikin bincikena akai: siyasa da addini. Idan kun ga hannuna a cikin ɗayan waɗannan biyun, wajen da na shahara ne, wato kan al’adun yaɗa labarai.
Misali, da na yi rubuce-rubuce da yawa na Zikirin Anfasu na ‘yan Ƙadiriyya, ba na yi a matsayin ɗaya daga cikin mabiyan ɗariqar ba, sai dai a matsayina na mai binciken harkar kiɗe-kiɗe – na mai da hankali kan yadda suke dukan jikinsu tare da motsa shi (bayan nazartar kyawawan ayyukan Margaret Kartomi kan dukan jiki yayin da take Maroko).
Hakazalika – don daidaita al’amura game da ɗariƙun Tijjaniyya da kuma Qadiriyyar – na rubuta zaman zikirin Tijjaniyya a Chiranci a cikin birnin Kano a wani ɓangare na nazari mai zurfi kan ayyukan addini. Duk yawancin ayyukan dai na ɗora su a kan YouTube domin amfanin al’umma.
Don haka na kan yi murmushi da nishaɗi a duk lokacin da mutane suke ƙoƙarin danganta ni a matsayin Baƙadire ko Batijjane. Ga shi kuma ba na ko ɗaya daga cikinsu.
A siyasance, ni ba na siyasa, ƙarewa ma ni ban damu da waye zai mulkin ƙasar nan ba. Ba na ma kaɗa ƙuri’a, tun da na yi sau ɗaya da daɗewa (a kan nacewar da abokina ya tilasta min na yi ), kuma na yi alƙawarin ba zan sake yi ba.
Amma fasahar wasan kwaikwayo ta jawo hankalina ga waƙoƙin zanga-zanga da kuma yadda ake gurfanar da mawaƙa a gaban kotuna a Kano. Inda har na rubuta maƙala akai mai taken , “Poetic Barbs”: Invective Political Poetry in Kano Popular Culture”, wanda na tabbata tana can a maƙale a wani wajen tun bayan lokacin da na gama da ita. A tunani shi ke nan.
A shekara ta 2014 na ci karo da wata waƙa da na ji daɗin sauraron ta. Ina kunnawa a kwamfutar tafi-da-gidanka (Laptop) sai wani ya nuna mamakinsa kan cewa ina sauraron waƙoƙin Dauda Adamu Abdullahi Kahutu, mai laƙani da Rarara.
Wannan shine karo na farko da na ji sunan. Waƙar “Zuwan Maimalafa Kano.” Ta ja hankalina ta hanyoyi biyu. Na farko, ginin waƙar da kuma isar da saƙon, abu ne mai kayatarwa tare da jan hankali.
Har nake ganin kamata ya yi a ce ya kasance mawaƙin rap, nau’in kiɗan da na fi so (tsohuwar tafiya irin ta DMX, 2Pac, Snoop Dogg, Ice Cube, Queen “The Equalizer” Latifah, ). A bayyane yake cewa Rarara yana rera waƙa, ba ya rubutawa ko karantawa daga takarda. Na biyu, ita ce waƙa mafi cikakken bayani da na ji a cikin salon waƙoƙin Hausa Afroop.
Tun sannan na fara zaƙulo shi da waƙoƙinsa. Don haka, tsawon shekaru bakwai da suka wuce, ina bin kowace waƙar da ya fitar ta amfani da hanyar Zambo.
To, menene waƙar Zambo? Zambo shine hanyar amfani da adabi ɗan zagin mutum ko wani abu ta hanyar amfani da kalamai na ɓatanci. Idan ku na so za ku iya kiran su da “zambo/shaguɓe”.
Zambo sau da yawa yana tare da munanan kalamai. Zambo ya rabu iri biyu: babba da Ƙaramin Zambo. Babban Zambo yana buƙatar amfani da harshe na yau da kullun da ƙirƙira, yayin da Karamin Zambo, a gefe guda, yake amfani da hotuna marasa kyau da kyamata.
Tun daga shekarar 2010, Rarara ya zama ƙwararren mashahurin mai waqoqin baka na Hausa. Ya na amfani da basirarsa wajen zagi, cin mutunci da kunyata duk wanda aka biya shi ya yi wa hakan. Ciki har da tsoffin iyayen gidansa da abokanai.
Wani tsari da ya samo asali a kai shine: Juyaw a mutum baya. A tarihi, wakarsa ta farko wacce ba ta da suka ita ce “Saraki Sai Allah” (lokacin da aka nada Gwamna Ibrahim Shekarau a matsayin Sardaunan Kano a shekarar 2010 da marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya yi).
A shekarar 2011 – bayan shekara guda – a lokacin da Shekarau ya ƙi naɗa ‘Ubangidan’ Rarara, Mataimakin Gwamna Abdullahi T. Gwarzo ya gaje shi. Nan ne ya sa ya rera waƙar – don dai kawai ya wulaƙanta Gwamnan, tare da cin zarafi da zage-zage ga iyayen gidansa daban-daban na baya.
Shekarau ya fuskanci cin zarafi kala-kala – sau da yawa, inda har ya kira Shekarau da DUNA baƙi. Babu wanda ya tsira daga zaginsa. Ya yi zage-zage sosai a cikin wakoki fiye da 39, tin daga 2014’s “Malam Ya Yi Rawa Da Alkyabba”, zuwa 2023’s “Tangal-Tangal.”
Na ga masu amfani da shafukan sada zumunta suna kiran Rarara kan cewa shi ba ɗan Kano ba ne, ya yi arziki a Kano ta hanyar wakokinsa, kuma yana zagin shugabannin Kano. Wannan duk gaskiya ne. Amman kuma duk da haka, ‘da ɗan gari a kan ci gari’ (maƙiyinka na gindinka).
Kimanin waƙoƙi uku ne kawai a cikin nazarin waƙoƙin Rarara da suka kasance ya buga su kyauta (wato, da ba a ɗau nauyin buga su ba). Duk sauran ‘yan siyasa ne daga Kano su ke biyan shi kafin ya yi su, don cin zarafin wasu ‘yan siyasar Kano. Rarara koyaushe yana maraba da masu ɗaukar nauyinsa dan ya yi waƙa domin sukar abokin hamayyarsu a siyasance.
Rarara ya kasance hamshaƙin mawaƙi mara tsari kuma mara ɗa’a. Nuna masa kuɗi, zai yabi babban abokinsa kuma ya zagi maƙiyin abokin. Ka ƙara shuna masa kuɗi, sai ya zagi abokin da ya yaba a baya, ya kuma yabi maƙiyin da ya zaga a baya. Shin kowa ya san cewa wanda akai wa waƙar “Ɗan Ƙaramin Sauro” (mai ban haushi) yana cikin “Banza Bakwai” (Seven Bastard)? Shi ma dai ba su ƙare da kyau ba, ko?
Ko ta yaya, irin salon waƙoƙin cin zarafi suka so zame masa bacin rai?. Inda a ranar 5 ga Afrilu 2023 lokacin da abokan hamayyarsa suka yi amfani da hoton mahaifiyarsa cikin kalmomi marasa daɗi kuma suka watsa shi a duk shafukan sada zamunta na zamani- tare da amfani da makamancin laƙabin sunan zagi da ya yi amfani da shi a kan ɗayansu.
Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya!
Don haka, maimakon a mayar da hankali kan aƙidar siyasa da alkawuran samar da kayan more rayuwa mai inganci ga al’umma, galibi ‘yan siyasa a Kano (kuma ni a ganina Kano, kamar yadda ta saba, ita ce kaɗai jihar da ta ke yin haka) suka fi maida hankali wajen tozarta mutane, da wulaƙanta su da kuma yin Allah wadai da ‘yan takara masu adawa da juna, da fitar da hoton ɗan siyasa da bai dace ba don kawai a hana a zaɓe shi. Rarara ya zam ludayin juyawa a wannan sigar.
Yana da daraja irin ta ’yan siyasar Kano a matsayin baƙo. Duk da hazakar waƙarsa, wani lokacin yana jawa kansa baƙin jini da yake kashe masa farin jini. Mawaƙa nawa ne daga Kano za ku iya tunawa suna zagi irin na Rarara ga ‘yan siyasar Kano? Biyu? Uku? Salonsu bai kai na Rarara ba. Akasin haka, ‘yan siyasa nawa ne daga Katsina suke biyan Rarara kudin zagin wasu ‘yan siyasar Katsina? Zan iya tunawa ɗaya kawai.
Tsananin yiwuwar ɗaukar matakin shari’a game da maganganun batanci kai tsaye, ‘yan siyasa sau da yawa suna samun sauƙin shigar da abin da na kira ‘karmamin siyasa’ don isar da saƙonsu na batanci ta hanyar shahararriyar hanyar rera waƙa.
Ta wannan hanyar, lokacin da gayyar tazo watsewa, mawaƙi shi kadai ne zai fuskanci shari’a -Mawaƙa marasa da’a irin su Rarara – wanda aka kama, amma ba a tuhume shi ba a 2014 kan “Zuwan Maimalafa Kano” – sun yarda su biya kuɗaɗe maƙudai dan a ƙara sakin su saboda in sukai wata waƙar, za su fanshe ta hanyar maƙudan kuɗaɗen da za su samu.
Kuma dan siyasar da ya jawo haka? Ba zai ma iya tuna waƙar da ta sa shi farin jini ba, bayan ya gama cin zabɓnsa. Har zuwa zagayowar zaɓe mai zuwa lokacin da zai kuma gayyato wani mawaƙin don ya sake rera masa wasu waƙoƙi masu inganci ta hanyar amfani da kalmomin yakin neman zabe masu tasiri a zukatan masu zaben.
Yadda zaka ka iya baiwa Rarara kariya shine na rashin furta sunaye a cikin zage-zagensa da cin mutuncin mutane, saboda babu sadara a cikin dokokin cin zarafin mutane na kundin mulkin Najeriya da ta bada dama ka iya kama shi a kan hakan. Kuma ya nuna cewa duk da yake haziƙin marubuci ne, yana bukatar fahimtar doka. Dalili kuwa saboda zagin da ya ke yi ta hanyar waƙoƙinsa a bainar jama’a sun yi waya.
Ya kan saka wani nau’i a waƙoƙinsa da ke kamanni da sunayen wasu ɗaiɗaikun mutane da ake iya gane su cikin sauƙi ko dai ta hanyar kamanninsu ko kuma ɗabi’unsu na yau da kullum a cikin jama’a, hakan na iya muzanta sunan mutumin da ya yi wa hakan. Don haka idan an yi niyya, kuma ba a yi kuskure ba kamar yadda furucin Rarara (daga waƙoƙinsa) ya kasance a bainar jama’a, mai shigar da ƙara wanda yasan abunda yake, zai iya daure Rarara saboda ɓata masa suna.
Ƙirƙirararrun waƙoƙi sau da yawa na iya samun kyakkyawar ginshiƙan su ta fuskar sanya ‘yan siyasa – ko masu son su. Suna iya haska fahimtar jama’a game da munanan ayyukansu, ko kuma aƙalla, halayensu mara sa kyau. Waƙoƙin zambo na Rarara a cikin zaɓaɓɓun waƙoƙin da na bincika, duk da haka, ba sa nuna ayyukansa a cikin lissafin jama’a ga ‘yan siyasa.
Manazarta daga Jamio’in ilimi sun yi watsi da Rarara da fasaharsa – kuma ina ganin yin hakan kuskure ne. Gaskiya ne, wasu za su ce waƙoƙinsa ba su da wata kima, ta hankali ko akida, amman dai ita kanta basirar tasa abar dubawa ce, ko da a kalamansa akwai mara sa kyau a ciki. Ba kamar sauran waƙoƙin da ke da salon isar da sakonnin siyasa ba, nasa ba waƙoƙin nuna fushi akan wani abu da ya damu al’umma ba ne, saboda basa nuna wani abu na aƙida.
Ba sa ilmantarwa, haskakawa ko kwatanta kowane fanni na al’adun siyasa. Suna nishaɗantarwa ne kawai – tare da zubar da mutuncin mutanen da yake suka a cikin su. Waƙoƙinsa sun haɗa da kalmomi balagaggu irin na mutanen karkara na Hausa wanda aka lulluɓe da zagi- kuma suna zama masu tayar da hankali ga ‘yan siyasa masu tunani irin na shi.
Bayan haka, wakokin Rarara ba za a iya kwatanta su ba, ta kowace fuska, da mawaƙan Hausa na gargajiya irin su Sa’adu Zungur, Mudi Sipikin, A wakilin Aliyu, Abba Maiyarru da Aminu Kano, wadanda akidar siyasa ta tarbiyyantar da fasaharsu, ko shakka babu. Mudi Sipikin, alal misali. ya yi amfani da wakarsa wajen ƙalubalantar tsarin mulkin mallaka. Wani ɗan wasalu Aliyu ya rubuta wakoki kai tsaye ga NPC. Abba Maiyarru ya rubuta wakar NEPU mai layi 10 wanda aka kama shi da Aminu Kano a tsakiyar shekarun 1950.
Zungur ya yi amfani da waƙarsa tun asali wajen gargaɗin sarakunan Arewa kan wajabcin kawo gyara, kamar yadda ya zo a cikin fitacciyar wakarsa ta Jumhuriya ko Mulukiya [Jamhuriya ko Masarautu]. A cikin wannan waƙa, ya yi kira da a warware matsalolin siyasa da zamantakewa bisa tushen koyarwar Musulunci da ake da su, tare da yin watsi da ra’ayoyin siyasa na kasashen waje.
Daga baya ya yi amfani da wakar wajen jan hankalin jama’a kai tsaye. Hakazalika, ɗaya daga cikin waƙoƙin farko da aka rubuta wa wata jam’iyyar siyasa ta Arewa ita ce ta Aminu Kano, ‘Ƴancin NEPU-Sawaba’ [Waƙar ‘Yanci ga NEPU-Sawaba], da aka buga 1953. Ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda akai maganganu na kishin kasa, Najeriya.
Duk da waɗannan, ina ƙalubalantar cewa a matsayin mu na masu bincike baikamata mu yi watsi da fasahar mawaƙan wannan zamanin ba. Amman goyon baya tare da ƙarfafawa da Rarara ya ke samu daga al’umma, hakane ya sa aka manta da irin su Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa) wanda ya zama abin alfahari ga duniyar masu nazarin adabin Hausa.
Sai aka karkatar da hankula kan Rarara. Duk wakar da Ala zai buga, sai ta kai sama da shekaru goma ana amfani da abinda ta ƙunsa, amman waƙoƙin Rarara ba kasafai suke wuce zamanin da aka fito da su ba. Nan take a ke mantawa da ita.
Duk da haka, kamar yadda muka yi ta-tashi-fadi lokacin da muke ta ƙoƙarin aiki akan Adabin Kasuwar Kano a shekarun 1990s, a lokacin da kowa ke ƙalubalantar abun, sai daga baya ne mutane suka fara aminta da batun, lokacin da suka ga wanda ba Bahaushe ba ya tashi tuƙuru yana yin aiki akan Adabin Kasuwar Kanon.
Dan haka, yanzu ma muna buƙatar mu yi rubuta akan abubuwan da ke faruwa fitattun al’adu, ciki har da irin na Rarara – tin wancan lokacin, kamar yadda na gani, Maikuɗi Kuzogi ne kaɗai ya mayar da hankali kan waƙoƙin Rarara guda biyu. Saboda haka. akwai buƙatar ƙarin masu nazari akai.
Duk lokacin da na zo daf da karasa rubutun binciken da nake game da Rarara, sai ya ƙara sakin wata waƙar da yake sukar wani tsohon ubangida ko abokin hamayyarsa. Daga baya, na jinkirta ci gaba da binciken har sai da ya soki mutane biyu, abunda kowa yake ta sauraro ya yi. Wadannan su ne shugaban kasa Muhammadu Buhari (Matsalar Tsaro) da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje (Lema ta sha ƙwaya). Da wakar ‘Hankaka’ da yake taba Ganduje a wakar ta Lema.
Kamar yadda na yi bayani, Rarara babban dan kasuwar yin wakoki ne ba tare da tsari ko akida ba. Maƙudan kuɗaɗen da yake samu za su zame masa amfani game da irin asarar da zai iya samu nan gaba a lokacin da ’yan siyasar Kano suka daina ba shi goyon baya don cin mutuncin juna (da kansu) idan ya koma amfani da fasaharsa ta hanyoyi masu inganci.
Godiyata ga tawagar masu taimaka min wajen aikin bincike, ƙarƙashin jagorancin amintaccen hadimina, Hassan Auwalu Muhammad – tsohon mai rubuce-rubuce.
Shi ne wanda ya fi juriyar yin rubuta wajen ɗaukar lokacin rubutawa/fassara min waƙoƙin da na fara aikin rubutun in da na sa a cikin wani labari mai zuwa kusan shafuka 40! Na yi shirin ɗora su a shafin sada zumunta a lokacin bazara idan ɗalibai sun fara hutun karatu. Zuwa lokacin wata kila barazanar Tanga-Tangal ta tsaya an shiga maganar shari’a gadan-gadan ta kusan tsahon shekaru hudu.