An Gudanar da Taron Zaman Sulhu da Ƙungiyoyin ’Yan Bindiga a Kankara

Daga Wakilanmu | Katsina TimesAn gudanar da wani taron zaman sulhu tsakanin al umma , sarakunan gargajiya, malamai da wasu daga cikin ƙungiyoyin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Kankara, Jihar…

Katsina City News August 16, 2026  ·  12:00 AM
| 32 Views
An Gudanar da Taron Zaman Sulhu da Ƙungiyoyin ’Yan Bindiga a Kankara
An Gudanar da Taron Zaman Sulhu da Ƙungiyoyin ’Yan Bindiga a Kankara

Daga Wakilanmu | Katsina Times

An gudanar da wani taron zaman sulhu tsakanin al umma , sarakunan gargajiya, malamai da wasu daga cikin ƙungiyoyin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Kankara, Jihar Katsina, a jiya Asabar.


An fara taron da misalin ƙarfe biyu na rana, amma an samu katsewa sakamakon hadari da ruwan sama, lamarin da ya sa aka tashi kafin a kammala taron. Duk da haka, an gabatar da jawabai tare da ɗaukar wasu muhimman alkawurra da matakai da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Daga cikin ’yan bindigar da suka halarci taron akwai Buzare daga Danmusa, Ado Aleru daga Zamfara, Sanusi Dan Dutsinma daga Kankara, Mustapha Babaro daga Kankara, Idi Malabaiye daga Kankara, Manore daga Safana, da kuma wakilan Idi Kwashen Garwa.


A ɓangaren gwamnati, akwai shugabannin ƙananan hukumomin Kankara, Faskari da Bakori, tare da wakili daga ƙaramar hukumar Malumfashi.

Advertisement

NRS Gateway

A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma, an samu halartar Hakimin Kankara, Mai Shari’a Adamu Bello mai ritaya, tare da dukkan magadansa, da kuma wakilin Kanwan Katsina, Hakimin Ketare tare da magadansa.

Haka kuma, limamai da malamai daga ɓangarorin Ɗariƙa da Izala sun halarci taron, inda suka gabatar da addu’o’i da nasihohi kan muhimmancin zaman lafiya da tsaro.

An gudanar da taron ne a wata gona da ake kira Gonar Bala Dabo, da ke kan hanyar Katoge, kimanin kilomita uku daga garin Kankara.

A yayin taron, shugabannin Fulani sun yi jawabai kan hanyoyin da za a bi domin tabbatar da dorewar zaman lafiya. Malamai sun gabatar da addu’o’i da nasihohi, yayin da masu unguwanni da sauran masu ruwa da tsaki suka yi jawabai na jan hankali tare da kira ga dukkan ɓangarori da su ba da haɗin kai domin kawo ƙarshen rashin tsaro.

Katsina Times za ta wallafa cikakkun bayanai da jawabai daga taron a shafukanmu na Facebook, ciki har da Katsina City News da Jaridar Taskar Labarai, da kuma sauran kafafenmu na intanet, ciki har da Katsina Times TV.


Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 9?