Matasa Sun Yi Kaiwa Tawagar Mataimakin Gwamnan Zamfara Hari da Jifa

Katsinatimes Wasu fusatattun matasa a garin Gwashe da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara sun yi wa Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni, ihu tare da zargin wasu daga cikinsu…

Katsina City News October 19, 2026  ·  12:00 AM
| 28 Views
Matasa Sun Yi Kaiwa Tawagar Mataimakin Gwamnan Zamfara Hari da Jifa
Matasa Sun Yi Kaiwa Tawagar Mataimakin Gwamnan Zamfara Hari da Jifa

Katsinatimes 


Wasu fusatattun matasa a garin Gwashe da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara sun yi wa Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni, ihu tare da zargin wasu daga cikinsu da kai hari kan ayarinsa, inda aka ce an lalata wata mota a yayin farmakin


Lamarin ya faru ne lokacin da mataimakin gwamnan ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummar yankin bayan wasu hare-haren ’yan bindiga da aka kai kan ’yan kasuwa a makon da ya gabata, wadanda rahotanni suka ce sun yi sanadin mutuwar jami’an tsaro da fararen hula tara, yayin da wasu suka samu raunuka.


Wani mazaunin yankin da ya zanta da jaridar Daily Trust bisa sharadin sakaya sunansa ya ce al’ummar yankin sun fusata da mataimakin gwamnan da gwamnatin jihar, saboda abin da ya bayyana a matsayin rashin damuwa da matsalolin tsaro da suke fuskanta.


Ya ce yankin na daga cikin manyan mazabu a karamar hukumar, amma tun bayan zaben 2023, babu wani babban jami’in gwamnati da ya sake ziyartar su domin duba halin da suke ciki.


“Fiye da shekaru uku da suka wuce, sun zo wajenmu a lokacin yakin neman zaben 2023. Tun daga lokacin, babu mataimakin gwamna ko wata tawagar gwamnatin jiha da ta sake ziyartar mu domin nuna damuwa kan matsalolin tsaro ko taimaka wa wadanda suka samu raunuka,” in ji shi.


Mazaunin yankin ya kara da cewa bayan hare-haren ’yan bindigar, al’ummar yankin sun shafe kwanaki shida a jere ba tare da fita sayen muhimman kayan masarufi ba.


Ya kuma koka kan karancin kayayyakin more rayuwa a yankin, yana mai cewa har dabbobi na amfani da wasu wurare a matsayin matsuguni.


Advertisement

NRS Gateway

Ya ce mata, yara, matasa da tsofaffi ne suka fito domin bayyana korafe-korafensu ga mataimakin gwamnan tare da nuna rashin gamsuwarsu da yadda gwamnati ke tafiyar da al’amuransu.


Sai dai wani mamba na tawagar mataimakin gwamnan, wanda shi ma ya yi magana bisa sharadin sakaya sunansa, ya musanta zargin cewa an kai hari kan ayarin.


“Abin da suke fada ba gaskiya ba ne. Mun kasance a wani wuri daban, kuma motar da suke ikirarin an lalata ta motar jami’an tsaro ce da ta samu matsalar inji. Daga baya aka ja ta aka tafi da ita,” in ji shi.


Wata majiya kuma ta shaida wa Daily Trust cewa tawagar mataimakin gwamnan tana da jami’an tsaro da dama, wadanda suka hana mutane kusantar wurin da tawagar take.


Sai dai majiyar ta ce: “Duk da haka, mun yi wa mataimakin gwamnan ihu tare da jifan ayarinsa.”


Da aka tuntubi Darakta Janar na Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Mataimakin Gwamnan, Shehu Adamu Gusau, ya ce bai kasance cikin tawagar ba, don haka ba shi da abin cewa kan lamarin.


Haka kuma, kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, bai yi nasara ba, domin ba a samu damar tuntubarsa ta wayar tarho ba.


Katsina Times

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 8?