BINCIKE NA MUSAMMAN: Mayar da Malaman Ɗariƙu da Mabiyansu Baya a Rarraba Mukaman Gwamnati: Lokaci Ya Yi da Ya Kamata Su Farka!

Daga Jaridun Katsina TimesKwanan nan, jaridun Katsina Times sun gudanar da wani bincike na musamman, inda suka gano tare da tabbatar da cewa malaman ɗariƙu da zuriyarsu sun kasance a…

Katsina City News October 13, 2026  ·  12:00 AM
| 23 Views
BINCIKE NA MUSAMMAN:  Mayar da Malaman Ɗariƙu da Mabiyansu Baya a Rarraba Mukaman Gwamnati: Lokaci Ya Yi da Ya Kamata Su Farka!
BINCIKE NA MUSAMMAN: Mayar da Malaman Ɗariƙu da Mabiyansu Baya a Rarraba Mukaman Gwamnati: Lokaci Ya Yi da Ya Kamata Su Farka!


Daga Jaridun Katsina Times

Kwanan nan, jaridun Katsina Times sun gudanar da wani bincike na musamman, inda suka gano tare da tabbatar da cewa malaman ɗariƙu da zuriyarsu sun kasance a baya wajen samun muƙaman gwamnati da za su iya taimaka musu wajen gina kansu da al'ummarsu a Jihar Katsina.

Binciken Katsina Times ya gano cewa an mayar da zawiyoyi da malaman ɗariƙun Sufaye baya a tsarin rabon muƙaman gwamnati da sauran damammakin da za su taimaka musu wajen bunƙasa rayuwarsu da al'ummominsu.

A cewar binciken, ana yawan tuna da malaman ɗariƙu ne idan lokacin gudanar da taron Mauludi ya zo, inda ake ba su gudummawa. Haka kuma, ana tuna da malaman Izala idan za su gudanar da nasu taruka, inda su ma ake ba su gudummawa.

Binciken ya kuma gano cewa, a wasu lokuta, ana amfani da tarukan karatun Alƙur'ani wajen jan hankalin malaman ɗariƙu, inda ake ba su kuɗin cefanen yini guda, ba tare da an samar musu da muƙaman da za su taimaka musu wajen gina kansu da mabiyansu ba.

Bambanci a Tsarin Rarraba Muƙamai da Kuɗaɗe


Binciken ya gano cewa akwai babban bambanci a yadda ake rarraba kuɗaɗen gwamnati da muƙamai tsakanin malaman Izala da malaman ɗariƙu.

A cewar binciken, duk lokacin da aka ware kuɗaɗe ga malaman ɗariƙu, ana ganin kamar an fi mayar da hankali wajen bai wa malaman Izala wani kaso mafi girma, wanda ke haifar da tambayoyi kan adalci da daidaito a tsarin rabon arzikin gwamnati.

Binciken ya nuna cewa malaman Izala suna samun muƙaman da za su iya taimaka musu wajen gina ƙungiyoyinsu da kuma samar da damammaki ga 'ya'yansu da sauran mabiyansu. Sai dai, a cewar binciken, ba a bai wa gidajen malaman ɗariƙu irin wannan dama yadda ya kamata ba.

Katsina Times ta gano cewa akwai muƙamai guda 14 waɗanda kowannensu zai iya zama wata dama ta gina mutane da dama, amma bisa bayanan da binciken ya tattara, muƙami guda ɗaya ne kawai aka gano ya samu hannun malaman ɗariƙu.

Muƙamai 14, Guda Biyar a Gida Ɗaya

Binciken ya kuma gano cewa daga cikin muƙamai 14 da aka danganta da tsarin rabon muƙamai ga ɓangaren Izala, guda biyar suna hannun mutanen da ke da alaƙa ta jini ko aure da shugaban ƙungiyar Izala ta jihar.

Waɗannan muƙamai, a cewar binciken, sun haɗa da na ɗansa, jikansa, surukinsa da ƙanensa. Sauran muƙamai uku kuwa, an danganta su da wasu daga cikin ɗalibansa na kusa.

Lokaci Ya Yi da Masana da Matasa Za Su Farka

Binciken Katsina Times ya gano cewa lokaci ya yi da 'yan boko, masana da sauran masu ilimi daga cikin malaman ɗariƙu za su farka, su zauna su yi nazari mai zurfi kan halin da suke ciki da kuma matakan da ya kamata su ɗauka domin kare muradunsu.

Yanzu da ake tunkarar lokacin zaɓe, ya kamata su haɗa kai su fuskanci duk masu neman muƙaman zaɓe da tambayoyi masu muhimmanci.

Me za ku yi mana idan muka ba ku goyon baya? Waɗanne muƙamai da damammaki za ku samar mana? Ta yaya za ku tabbatar da cewa an kare mutuncinmu, an kuma ba mu damar bayar da gudummawa wajen ci gaban jihar?

Ya kamata matasan ɗariƙu su fuskanci masu neman ƙuri'unsu da murya ɗaya, tare da bayyana buƙatunsu da kuma neman tabbaci kan yadda za a biya buƙatun al'ummominsu.

Haka kuma, ya kamata masu ilimi da masana daga cikin malaman ɗariƙu su fahimci cewa rashin haɗin kai da rashin tsayawa tsayin daka wajen kare muradunsu na iya sa su rasa damammaki masu muhimmanci a siyasance da zamantakewa.

Advertisement

NRS Gateway

Binciken ya nuna cewa akwai haɗarin da zai iya tasowa idan aka ci gaba da wannan yanayi, inda malaman ɗariƙu da mabiyansu za su iya rasa tasirinsu a cikin al'ummominsu, duk da irin gudummawar da suke bayarwa a fannin addini da zamantakewa.

Gyara Ba Zai Zo Cikin Dare Ɗaya Ba

Katsina Times ta gano cewa bambancin da aka samu a tsarin rarraba muƙamai da damammaki tsakanin waɗannan ɓangarori ya yi yawa, kuma ko da an fara ɗaukar matakan gyara tun yanzu, zai iya ɗaukar shekaru kafin a samu daidaito.

Binciken ya kuma nuna cewa malaman Izala sun yi amfani da damar haɗin kai da tsarin ƙungiyarsu wajen samun wasu damammaki. Sai dai, bisa hasashen binciken, akwai buƙatar a yi nazari kan ko ana samun daidaito a zahiri wajen rabon muƙamai da sauran damammakin gwamnati, ko kuwa akwai ɓangarorin da ke samun fifiko fiye da sauran.

Saboda haka, ya kamata malaman ɗariƙu su sake nazarin matsayinsu, su ƙarfafa haɗin kai, su kuma tsara dabarun da za su taimaka musu wajen kare muradunsu a siyasance ba tare da yin watsi da koyarwar addininsu da manufofinsu na zaman lafiya ba.

Waɗansu Ƙungiyoyi Sun Riga Sun Ɗauki Matakai

Binciken ya kuma lura cewa wasu ƙungiyoyin addini, ciki har da mabiya mazhabar Ja'afariyya, sun daɗe suna gudanar da ayyukansu bisa tsare-tsare da jadawalin da aka tsara tun da farko. Wannan tsari ya taimaka wajen samar da wasu matakai na tafiyar da al'amuransu.


Sai dai, abin da binciken ya jaddada shi ne cewa malaman ɗariƙu na buƙatar yin nazari kan yadda za su inganta tsarinsu, su fahimci muhimmancin wakilci a hukumomin gwamnati, sannan su samar da dabarun da za su taimaka wajen tabbatar da cewa an yi la'akari da muradunsu wajen rarraba muƙamai da damammaki.

Saƙo ga Malaman Ɗariƙu: Ku Farka Kafin Lokaci Ya Ƙure!

Babban saƙon da binciken Katsina Times ke isarwa ga malaman ɗariƙu, masana, matasa da sauran mabiyansu shi ne cewa lokaci ya yi da za su farka, su yi nazari, su haɗa kai, su kuma tsara makomarsu.

Lokacin zaɓe dama ce ta tambayar 'yan takara abin da za su yi wa al'ummomi, ba wai lokacin karɓar alƙawura kawai ba.

Ya kamata malaman ɗariƙu su nemi tsarin da zai tabbatar da adalci, wakilci da daidaito wajen rabon muƙamai da damammakin gwamnati, kamar yadda ya kamata a yi wa sauran ɓangarorin al'umma.

Ku farka tun kafin ku yi fargar jaji!

Wannan shi ne saƙon da Katsina Times ke isarwa bisa abubuwan da ta gano a bincikenta na musamman.


Katsina city news Facebook page 

Katsina city news  Facebook group 

Jaridar Taskar labarai Facebook page 

YouTube TV...katsina times 

@ www.katsinatimes.com 07043777779

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 9?