Kungiyar matan jam'iyyar adawa ta PDP mai rajin dawowar jam'iyyar Mulki a jihar a zabukan shekarar 2027 mai suna "Shama Kamshi 34 LGA's Women Initiative Supporting PDP 2027" ta shirya taron wayar da kan mata game da Jam'iyyar ta PDP tare da raba masu fama-faman rajistar shiga shirin koyar da sana'o'i kyauta.
Taron wanda ya samu halartar daruruwan mata da suka fito daga mazabu daban-daban a fadin jihar, an gudanar da shi a ranar Lahadin nan 22 ga Yuni, 2025, a hedikwatar jam'iyyar ta jihar Katsina.
A yayin da take jawabi a taron, shugabar kungiyar, Ambasada Shamsiyyar Mustapha ta bayyana taron a matsayin na tabbatar wa iyaye mata da sauran al'ummar jihar Katsina baki daya da cewar jam'iyyar ta PDP na nan da ruhinta a jihar, inda ta ce "Tafiya kuma yanzu aka fara."
Shamsiyya, ta kuma bayyana cewar jita-jitar da ake yadawa na cewar wai jam'iyyar PDP ta mutu murus a jihar labarin kanzon kurege ne, inda ta jaddada cewar jam'iyyar na nan da dukkan abin da aka san ta da shi musamman na shuka alkhairai wanda al'ummar jihar ba za su taba mantawa ba.
Daga karshe ta hori matan jihar da su fito su nuna karfi da 'yancinsu a zabuka masu zuwa, inda ta bayyana jam'iyyar ta PDP wadda Sanata Yakubu Lado ke a matsayin madugunta a jihar a matsayin Jam'iyya abar maida wa biki.
Daga bisani, a taron, Ambasada Shamsiyya ta bada wasu kyaututtukan girmamawa ga wasu jiga-jigan jam'iyyar a matakin jiha, tare da kaddamar da Fama-faman koyar da Sana'o'i wasu daga cikin matan, a yayin da ta bayyana cewar kowacce mace da ta halarci taro za ta karbi nata a hannun wakiliya a mazabarta.
Wadanda suka halarci taron da gabatar dda jawabi a wajen sun hada: Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Honorabul Nura Amadi Kurfi wanda ya samu wakilcin, Sanusi Abdullahi Fari, Shugabar Matar jam'iyyar ta jiha, Honorabul Husaina Ahmad Daura da sauransu.