Daga NASIR S. GWANGWAZO
Daga dukkan alamu Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki matsaya kan wanda zai tsaya wa Jam’iyyar APC takarar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Bagwai da Shanono a babban zaben 2026, inda yake kokarin mika takarar ga wanda ba shine akasarin al’iummar yankin suke so ba, duk da cewa, mazabar tana da mai neman takarar wanda duk Nijeriya an yarda da tasirinsa a Majlisar Dokoki ta Kasa, wato tsohon dan majalisa, Hon. Farouk Lawan.
Sunan Hon. Farouk Lawan ba bakon abu ba ne a siyasar Nijeriya, ballantana ta Jihar Kano, mahaifarsa, saboda tasirin da ya yi a Majlisar Wakilai lokutan gwamnatoci daban-daban da suka shude kama daga ta Obasanjo, Yar’Adua zuwa ta Jonathan, inda har aka rika yi masa lakabi da ‘Mr. Integrity’ ko ‘Ka Fi Speaker’.
A lokacin da Farouk Lawan ke sharafinsa a Majalisar Dokoki ta Tarayyar Nijeriya, kowa ya yarda cewa, majalisar tana da nagarta fiye da yadda ake gani bayan da ba ya nan daga zamanin gwamnatin Buhari zuwa yanzu, saboda yadda a lokutansa Majalisar Wakilai ke iya taka wa bangaren zartarwa birki a duk lokacin da aka nemi kauce hanya.
Amma sai dai hakan ba ya nufin a lokacin da Faruku ke majalisa, ita majalisar ba ta mara wa bangaren zartarwa baya kan kyawawan manufofin da suka zo da su a koyaushe, illa dai kawai ana yin abun ne cikin mutuntaka da bin doka da ka’idojin aiki. Babban misali shine, yadda aka zauna lafiya tsakanin Majalisar Dokoki da bangaren zartarwa a zamanin Marigayi Yar’Adua, gwamnatin da ake kallo a matsayin mafi nagarta da aka taba yi tun bayan kafa wannan Jamhuriya ta Hudu.
Wannan tsari na daga cikin dalilan da suka sanya Shugaba Tinubu ya yi yafiya ga Hon. Farouk Lawan bayan da ake ganin gwamnatin Jonathan ta shafa masa kashin kaji, sannan gwamnatin Buhari ta kasa yi masa abin da gwamnatin Tinubu ta yi na yafiya. Yafe wa Hon. Farouk Lawan na daya daga cikin abubuwan da Tinubu ya yi wa ’yan Arewa, wadanda ba za a taba manatawa da su ba, saboda Shugaba Tinubu yana da basirar gane cewa, samun irin su Faruku a Majalisar Dokoki zai taimaka matuka gaya wajen dawo da martabar Nijeriya a idanun duniya ba tare da kace-nace tsakanin bangaren zartarwa da majalisa ba. Bai dace Gwamnan Kano ya hana wa Nijeriya samuwar hakan ba.
A yanzu da ake ganin al’amura sun cakude kan yadda ake tafiyar da Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu, manazarta da dama suna kallon hakan yana da nasaba da yadda Majalisar Dokoki ke tafiyar da dangantakarta da bangaren zartarwa, inda wasu ke ganin cewa, majalisar ta kasa ba ta taimaka wa bangaren zartarwa wajen aiwatar da kyawawan manufofin da Gwamnatin Tinubu ta tsara har ma ake kallon ta a matsayin gwamnatin da ta yi bakin jini a idanun ’yan kasa, alhali wasu manufofin da ta ke gabatarawa za a ga amfaninsu a nan gaba, amma yadda ake gabatar da su a majalisa kuma ake amincewa da su kai tsaye ne yake janyo surutai a tsakanin ’yan Nijeriya, musamman ’yan Arewa. Wannan ya sanya ake kallon majalisa a matsayin ’yar amshin Shata.
Don haka lallai ya dace a samu kwararru a Majlisar Dokoki ta Kasa, wadanda za su iya amfani gogewarsu wajen ganin an saisaita al’amura, kamar yadda ya faru a lokacin Yar’Adua, domin ba koyaushe ba ne fada da bangaren zartarwa ke amfanar ’yan kasa.
Dakile dawowar Farouk Lawan zuwa majalisa a wannan lokaci zai kawo cikas ga manufofin Tinubu na ganin an dawo da martabar Gwamnatin Tarayya da ita kanta majalisar, kuma koma-baya ne ga jihar Kano da Arewa, domin akwai bukatar samun gogaggu, wadanda va dolaye ba ne, a Majalisar Dokoi kuma dan majalisa daya tamkar da goma irin Faruku, don saita al’amura.
Hakika lallai ya wajaba ga Gwamna Abba Yusuf ya fahimci Shugaba Tinubu akan batun nan na tsayar da dan takara kuma ya gane alkiblar al’ummar mazabar Bagwai da Shanono da Jihar Kano da Arewa da ma Nijeriya bakidaya!
Rigingimun da ake haifarwa da sunan masalaha a wajen tsayar da ’yan takarar APC, tabbas wagegiyar kofa yake budewa ga ’yan adawa, wadanda a shirye suke su yi amfani da damar wajen kifar da gwamnatin jihar!
Nasir Gwangwazo ɗan jarida ne mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya.