Sanata Yakubu Lado ba ya biyan haraji a Katsina — Shugaban Hukumar Tattara Haraji

Mu’azu Hassan | Katsina TimesShugaban Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Katsina, Alhaji Muhammad Isiyaku, ya bayyana cewa Sanata Yakubu Lado Danmarke, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, ba ya biyan…

Katsina City News August 08, 2026  ·  12:00 AM
| 29 Views
Sanata Yakubu Lado ba ya biyan haraji a Katsina — Shugaban Hukumar Tattara Haraji
Sanata Yakubu Lado ba ya biyan haraji a Katsina — Shugaban Hukumar Tattara Haraji


Mu’azu Hassan | Katsina Times

Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Katsina, Alhaji Muhammad Isiyaku, ya bayyana cewa Sanata Yakubu Lado Danmarke, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, ba ya biyan harajinsa a Jihar Katsina.


Alhaji Muhammad Isiyaku ya ce, a halin yanzu, babu wani fayil a hukumar da ke nuna cewa Sanata Yakubu Lado yana biyan haraji a Jihar Katsina.


Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da Katsina Times, inda ya ƙara da cewa fayilolin wasu ’yan siyasa, ciki har da Sanata Ahmad Babba Kaita, Dakta Mustapha Inuwa da Malam Dikko Umar Radda, sun daɗe a hukumar, kuma suna biyan haraji a jihar kamar yadda doka ta tanada.


Ya ce, haka kuma, wasu ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban da kuma ’yan takara a wasu jam’iyyun suna biyan harajinsu a Katsina, sannan hukumar tana ba su takardar shaidar biyan haraji.


Sai dai Katsina Times ta tuntubi wani na kusa da Sanata Yakubu Lado kan zargin cewa baya biyan haraji a Katsina. Mutumin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya musanta zargin, yana mai cewa Sanata Lado yana biyan haraji kamar yadda doka ta tanada.


A cewarsa, dokar haraji ba ta ce dole ne mutum ya biya haraji a Katsina ba. Ya ce Sanata Lado yana kauce wa biyan harajinsa a Katsina ne saboda shi ɗan takarar adawa ne, kuma ana ƙoƙarin ganin an samu wata kafa ta zarge shi.


Ya ƙara da cewa Sanata Lado na iya zuwa ya biya harajinsa a Katsina, kuma a jinkirta ba shi takardar shaidar wankewa ta biyan haraji. Sai dai ya yi zargin cewa wasu daga cikin  abokan siyasa a jam iyya daya da Sanata Lado da suka je neman takardun shaidar biyan haraji sun fuskanci matsaloli kafin a ba su takardun.

Advertisement

NRS Gateway


A wani ɓangare na hirar, Shugaban Hukumar Tattara Harajin ya yabawa wasu attajirai da ya ce suna taka muhimmiyar rawa wajen biyan haraji.


Ya ambaci Sanata Sama’ila Mamman Kurfi da Sanata Ibrahim Ida, inda ya ce: “Waɗannan dattawan Allah, Allah ya saka musu da alheri.”

Ya ce a duk shekara, maimakon su biya harajinsu ga Gwamnatin Tarayya ko wata jiha, suna zuwa Jihar Katsina ne domin biyan harajin bisa ƙa’idar da ta dace da dukiyarsu.


Ya kuma yaba wa Alhaji Dahiru Barau Mangal, inda ya ce ribar kamfanoninsa  tana daga cikin abubuwan da ake lissafawa wajen biyan haraji.

Korafe-korafe kan wasu kamfanoni

Shugaban hukumar ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda wasu manyan kamfanoni da wasu otal-otal da wuraren saukar baki ba sa cika biyan harajin da ya kamata.


Ya bayar da misalin katafaren shagon kasuwanci mai suna Green House, inda ya ce har yanzu hukumar na tattaunawa da masu shagon kan adadin harajin da ya kamata su biya.


Ya ce hukumar na kuma jiran umarnin kotu domin ta fara wani gagarumin aiki kan wasu manyan kamfanoni da bankuna da ke Jihar Katsina, domin tabbatar da cewa suna biyan harajin da doka ta tanada.


Katsina Times  za a wallafa cikakkiyar hirar da akayi  yi da Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Katsina ranar Litinin mai zuwa, a dukkanin shafukan yanar gizon jaridar na Katsina times

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 9 + 2?