KIWON LAFIYA: KYANDA (MEASLES)
- Katsina City News
- 22 Aug, 2024
- 431
Ita dai kyanda cuta ce wadda ake dauka daga mutum zuwa mutum. Idan cutar ta kama mutum, za ta haifar da wanzuwar kuraje a jiki, tare da mura da shakewar murya. Haka nan kuma, cutar ta fi kama kananan yara, musamman wadanda suke kasa da shekara biyar (5). Idan mutum ya taba fama da cutar, ba zai sake yin ta ba har tsawon rayuwarsa. Cutar na kasancewa cikin jikin mutum har tsawon kwanaki goma zuwa sha biyar (10-15) kafin ta fara nuna alamominta.
ALAMOMIN KYANDA
Alamomin kyanda sun kasu kashi uku kamar haka:
Kashi na Farko:
1. Zazzabi
2. Ciwon kai
3. Tari da mura
Wadannan alamomi ana iya ganin su kwanaki uku (3) bayan kamuwa da cutar.
Kashi na Biyu:
1. Zazzabin zai kara tsananta
2. Idanu za su yi ja, su rika fitar da kwantsa
3. Atishawa
4. Lebe zai yi ja wur (wannan alama ita ce tabbatatta, kuma ga mai fama da ciwon kyanda ne kawai ake samun irin wannan alama).
5. Wanzuwar kuraje wanda za su fara fitowa a goshi, cikin kai, bayan kunnuwa, fuska, kugu, da kafafuwa
6. Shakewar murya (a sakamakon wanzuwar kurajen a makoshi)
Kashi na Uku:
1. Sannu a hankali kurajen sai su cika jiki
2. Bayan kwanaki uku zuwa hudu (3-4) da fitowar kurajen sai su fara kyankyashewa
HANYOYIN DA AKE IYA DAUKAR CUTAR
Ana iya daukar kyanda ta hanyoyi guda biyu kamar haka:
1. Ta hanyar amfani da kayan da suke dauke da kwayoyin cutar.
2. Ta hanyar shakar gurbataccen iska.
ILLAR KYANDA
Kyanda na haddasa matsaloli kamar haka:
1. Wuya zai kumbura amma idan aka taba babu zafi.
2. Ciwon guiwa.
3. Kurumta (mutum ya rasa ji).
4. Bari ga mata masu juna biyu.
5. Haihuwar jinjiri nakasasshe.
YADDA AKE GANE CUTAR
Ana gane kyanda ta hanyoyi kamar haka:
1. Lura da alamomin da aka zayyana, musamman wanzuwar kuraje da kuma fitar kaluluwa a wuya.
2. Hanyar awo na jini a asibiti domin gano kwayar cutar.
YADDA ZAKA KIYAYE AUKUWAR CUTAR
1. Yin allurar rigakafi.
2. Idan aka taba fama da cutar sau daya, ba za a kara kamuwa da ita ba.
A guji barin yara cikin dauda yayin da suke fama da ciwon, domin tsabta ita ce lafiya. Saboda haka, a kula da bin umurnin likita da ma'aikatan lafiya, da kuma bayar da magani kamar yadda aka rubuta. Da fatan Allah Ya sa mu dace. Amin.
Daga Littafin Kula da Lafiya Na Safiya Ya'u Yemal