Auwal Isah | Katsina Times
Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), reshen jihar Katsina, ta gudanar da taron jin ra’ayin al’umma tare da masu ruwa da tsaki kan mummunar dabi’ar nan ta rubutu a jiki da kayan makaranta wanda dalibai ke yi bayan kammala Makaranta. Dabi’ar wadda ake kira da “Sign-out/Marker day” ta fara zama ruwan dare a sassan Nijeriya, abin da hukumar ta ce ya saba da mutunta ilimi, al’ada da kuma addininmu.
Baya ga batun “Sign-out”, taron ya kuma tattauna kan wasu batutuwa guda huɗu: Manufofi da tsare-tsaren gwamnati, Daratta alamomin ƙasa, Yanayin tsaron al’umma, da kuma Matsalar ambaliyar ruwa.
Da yake jawabi a taron, Daraktan NOA na Katsina, Malam Mukhtar Lawal Tsagem, ya ce hukumar ba wai kawai tana wayar da kan jama’a ba, har ma da sauraren ra’ayoyin jama’a da tattaunawa da su, yana mai cewar taron ya bada dama ga jama’a su gabatar da tambayoyi da shawarwari, wadanda za a isar wa shugabanni don yin duba.
“Wannan shiri a yanzu ana gudanar da shi a kowace jiha. Duk abin da aka tattauna za a tattara shi, a aika wa shugabanni, su nazarta su kuma tace don amfanin ƙasa,” in ji shi.
Shi ma Daraktan Shirye-shirye na NOA ta ƙasa, Mista John Bala Asate, ya ce an shirya wannan taro ne sakamakon ganin yadda ɗabi’un al’umma ke ta6ar6rewa a hankali. Ya ce hukumar ta mai da hankali kan fannoni biyar da suka kunshi: Wayar da kan jama’a kan shirye-shirye da manufofin gwamnati, Kare al’umma daga ambaliya da bala’o’i, Tsaron ƙasa da al’umma, Girmama alama da tambarin ƙasa, da kuma Dakile dabi’ar “Sign-out” a makarantu.
A cewarsa, "Dabi’ar da dalibai ke yi bayan kammala makaranta ta ‘Marker-day’ ko ‘Sign-out’ ba ta dace da mutunta ilimi ba, kuma gwamnati ta damu ƙwarai da gaske da wannan hali."
Ya kuma yi bayani kan wasu shirye-shiryen gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ya ce don rage radadin rayuwa ne bayan cire tallafin man fetur. Ya bayyana Tallafin kuɗi na musamman ga al’umma, Asusun Renewed Hope Infrastructure Fund don gyara makarantu a karkara, Conditional Cash Transfer ga talakawa, Shirye-shiryen tallafin kasuwanci irin su TraderMoni da EmpowerMoney, da kuma tallafin karatu ga ɗaliban manyan makarantu (NELFUND) da sauransu, a matsayin misalai.
A nasa jawabin, Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, wanda Hakimin Gundumar Shinkafi, Turaren Sarkin Katsina Abdurrashid Abubakar ya wakilta, ya yaba da ƙoƙarin NOA wajen wayar da kan jama’a, yana mai umurtar iyaye da sauran jama’a da su bada cikakken goyon baya ga hukumar domin samar da tarbiyya da 'yanƙasa nagari.
A yayin taron, mahalarta sun gudanar da musayar ra’ayi, tambayoyi da amsohi, bayar da shawarwari wanda iyayen dalibai, wakilan ƙungiyoyi, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar.