An bankaɗo Yadda Aka Sace $6.2m Daga CBN A Cikin Sa'o'i 24 Kuma Aka Kasafta ta
- Katsina City News
- 19 Jun, 2024
- 313
Jimillar kuɗi har Dala 6,230,000 da ake zargin an sace daga Babban Bankin Najeriya (CBN) a ranar 8 ga watan Fabrairun shekarar 2023, an raba su tare da saka hannun jari a kasuwancin gidaje da kuɗin kamar yadda wani kundin binciken kotu ya nuna.
Dala Miliyan 6.2 a cewar tawagar binciken Shugaban ƙasa ta Musamman karkashin jagorancin Jim Obaze da suka binciki tsohon Gwamnan Babban bankin ƙasa CBN Godwin Emefiele, an gano cewa an cire kuɗaɗen ne daga taskar bankin ƙasa da sunan biyan masu sanya ido kan zabe a zaben 2023.
Emefiele dai a halin yanzu yana fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume 20 da Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Tu’annati (EFCC) take yi a kansa.
Ana zarginsa da aikata laifin cin amana, da hadin gwiwar karya da kuma samun kudi ta hanyar karya a lokacin da yake rike da mukamin Shugaban Babban bankin ƙasa.
A cikin takardun kotun, masu binciken sun bayyana satar a matsayin wani aiki na cikin gida da ake zargin galibin jami’an bankin CBN ne tare da hadin gwiwar wasu mutane biyu da aka bayyana sunayensu, Adamu Abubakar da Imam Abubakar suka gudanar.
A cewar takardun, masu binciken sun yi ikirarin cewa babban mataimakin Emefiele na Musamman Odoh Eric Ocheme ya karbi dala 3,730,000 na kudaden, inda wasu mutane su uku ya raba masu sauran dala Miliyan 2 da dubu 500 (2,500,000).
An ce Ocheme ya bayar da hujjar da ta sanya kason nasa ya zarce nasu cewa sai ya biya wasu kuɗaɗe domin gyaran aikin ga wasu jami'an babban bankin.
A daya daga cikin takardun kotun an bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda suka samu kuɗin sun zuba hannun jarin da aka kiyasta zai kai kimanin Naira biliyan 14 a cikin wani kasuwancin gidaje wanda yanzu haka an kwato wani bangare daga cikin kason nasu.
An ruwaito mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan ya ce “Mun fara bincike kan lamarin kuma mun samu kwafin takardar cire kudin da kuma takardun da babban bankin Najeriya ya rubuta a ranar 07/02/2023 da kuma 31/01/2023, da kuma Kwafin wasikar Jibril Abubakar mai kwanan wata 2/01/2023 wanda aka ce Muhammadu Buhari ya rubutawa Boss Mustapha, da wasika mai kwanan wata 20/01/2023, sai kuma wadda Boss Mustapha ya rubutawa Mista Godwin Emafiele wanda da ita ce babban bankin Najeriya reshen Abuja ya dogara da shi wajen amincewa da cire kuɗaɗen.
Binciken da aka gudanar a ofishin shugaban kasa da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya ya nuna cewa wasikun da ake zargin Muhammadu Buhari da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) Boss Mustapha ne suka rubuta ba daga Ofisoshin su suke ba, yayin da Jibril Abubakar wanda aka yi amfani da katin shaidarsa wajen fitar da kudaden da ake magana a kai ba ma ma’aikacin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ba ne.
Mun ziyarci gidan gyaran hali na Kuje Correctional Centre inda muka yi hira da Godwin Emefiele wanda bincike ya nuna cewa shine ya sanya hannu a takardun lokacin yana shugaban Babba bankin, amma kuma sai ya musanta ganin takardar ballantana kuma Maganar amincewa da ita.
Haka kuma mun damke wasu ma’aikatan babban bankin Najeriya da ke da alaƙa da binciken, wadanda suka musanta cewa suna da hannu a wannan aika-aika kafin daga bisani muka kama Bashirudeen Maishanu wanda ya tabbatar da hannun su a badaƙalar, sannan ya kara da cewa yana da hannu a wannan aika-aika wanda a cewar sa shi ne ya aikata da kansa tare da sauran wadanda ake zargi Adamu Abubakar, da Imam Abubakar, da kuma Odoh Eric Ocheme.
Bashiru Maishanu ya kara da cewa shi kansa, da Adamu Abubakar, da Imam Abubakar sun raba kudi dala 2,500,000 na kudaden da aka sata, yayin da cikon na uku Odoh Eric Ocheme wanda ya kasance ma’aikacin babban bankin Najeriya ne ya samu dala 3,730,000 00 yana mai cewa yana da wasu bukatu da zai warware dangane da harƙallar a CBN.
Bashirudeen Maishanu ya kuma kara da cewa shi da wadanda ake kara na daya da na biyu sun hada hannu wajen zuba hannun jari na dalar Amurka kwatankwacin Naira 1,440,000,000.00 a kasuwancin gidaje na kamfanin Afrolyk Global Ltd.
Manajan Daraktan kamfanin Afrolyk Ltd Aminu Lawal da aka kama ya tabbatar da hannun jarin Bashirudeen Maishanu Adamu Abubakar da Imam Abubakar kuma tuni ya mayarwa tawagar masu bincike na musamman kuɗi Dala 200,000.00 a matsayin wani bangare na kuɗaden da suka zuba.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa