TAKAITACCEN TARIHIN MADAWAKIN KANKIA MUHAMMADU BATURE DA DIYAR SHI ATTAJIRA HAJIYA BAIKA - Yulaks KY
- Katsina City News
- 24 Apr, 2024
- 840
Malam Isiyaku wani shahararren malamin addinin Muslunci ne wanda asalin shi yazo ne daga ƙasashen Arewacin Afrika ana kyautata zaton shi Tuareg ne, ya zauna a Bumbum ta ƙasar Maiaduwa dake Daura inda ya rayu na tsawon lokaci. Malam Isiyaku yana da 'ya'ya guda biyu maza, Muhammadu da Tukur. Shi Muhammadu sana'ar safarar dawaki yakeyi, ya sawo ya saida daga gari zuwa gari musanman daga Bumbum zuwa Daura. Shi kuma ɗanuwan shi Tukur malami ne kamar mahaifin su.
Bayan wani lokaci sai Allah Ya yi ma Malam Isiyaku mahaifin su Muhammadu (wanda akan kira shi da laƙabin Bature) da Malam Tukur rasuwa a garin na Bumbum. Bayan rasuwar mahaifin na su, sai Muhammadu Bature da Malam Tukur sukayo hijira daga garin na Bumbum suka dawo garin Kankia tare da Iyalan su. Malam Muhammadu Bature shima ya tafo tare da matar shi mai suna Altine.
Bayan sun iso Kankia, Malam Tukur yaci gaba da hidimar shi ta malanta, shi kuma Bature sai yaci gaba da sana'ar shi ta safarar dawaki. A wannan zamani, tsakiyar ƙarni na sha takwas, Muhammadu Bature sai ya zamanto shi ke kawo ma Kankiyan Katsina na wannan lokaci dawaki duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Ana haka, ƙarshe sa Kankiyan ya naɗa shi sarautar Madawakin Kankiya. A bincike na ina sa ran anyi wannan naɗi a zamanin Kankiya Durbi Gidado (1865-1868) kuma Madawaki Muhammadu Bature yaci gaba da riƙe sarautar shi har zamanin Kankiya Bebeji Muhammadu Bello(1889-1894).
Madawaki Muhammadu Bature yaci gaba da hidimar shi ta sana'ar dawaki da kuma kula da dawakin Kankiya a matsayin shi na Madawakin Kankiya har zuwa shekarar 1891 lokacin da Allah yayi nashi rasuwa. Kafin rasuwar shi, Madawaki Bature yana da 'ya'ya guda takwas, kuma daga cikin 'ya'yan nan takwas akwai Fatima wadda akafi sani da sunan Ɓaika, ita ce ɗiya ta biyar wajen Madawakin Kankiya Muhammadu Bature da Altine mahaifiyar ta.
An haifi Hajiya Fatima Ɓaika a shekarar 1886 a garin Kankia. A nan kankia aka yaye ta har takai kusan shekaru biyar zuwa shidda. Ita dai Hajiya Ɓaika shahararrar attajira ce da akayi a ƙasar Katsina, tun daga nan kasashen Hausa har zuwa faɗin nahiyar Afrika ta yamma.
Bayan rasuwar mahaifinta watau Madawaki Muhammadu Bature, sai ɗanuwan mahaifinta Malam Tukur ya ɗauke ta ya rike tare da sauran marayun yan'uwan ta yaci gaba da kula dasu. Sai dai ba'a daɗe ba bayan rasuwar Madawaki Bature sai Malam Tukur ya tattara iyalan nan gaba ɗaya yayi hijira daga garin Kankia zuwa birnin Katsina inda ya safka a Unguwar nan da ake kira Darma. A unguwar Darma ne Wakilin Kudu ya bashi masafki kuma yaci gaba da hidimar shi ta malantaka. Wannan shine dalilin komawar Hajiya Ɓaika garin Katsina tare da babanta Malam Tukur.
Bayan Ɓaika ta girma sai aka aurar da ita ga wani ɗalibin Malam Tukur mai suna Abba Saudi a shekarar 1900. Hajiya Fatima Ɓaika dai haifaffar Kankia ce daga zuriyar Madawakin Kankiya Malam Muhammadu Bature. Hajiya ta kasance shahararrar yar kasuwa kuma attajira a zamanin ta, wadda sunan ta ya kai ko ina. Bincike ya nuna a tsakanin shekarun 1930 zuwa 1960 babu mai kuɗinta a ƙasar Katsina. Hajiya Ɓaika ta rasu a shekarar 1966 kuma ta bar iyali. Daga cikin 'ya'yan ta akwai fitattun yan kasuwa irin su Alhaji Iron Baba (wanda keda gidan mai IBS na Kankia), akwai Alhaji Madugu Darma, da Alhaji Ɗahiru Saude (AD Saude), da Alhaji Raben Ɓaika da sauran su. Allah Ya jiƙan magabatan mu.
Yusuf Lawal Kankia
Makaman Kankia
#yulaksky
08065595555
-------------
Note: Akwai references Amma zasu fito a littafin da Nike cikin rubutawa ne.
#yulaksky