AN KORI SAKATAREN KARAMAR HUKUMAR KURFI,DA KANSILOLIN DA BA ZABBABU BA.
- Katsina City News
- 18 Apr, 2024
- 386
Daga Fatima Hassan. Katsina Times
Wata takarda da ke yawo a bisa yanar gizo mai dauke da sanya hannun Rabi u Ibrahim kaita, mukaddashin daraktan gudanarwa na karamar hukumar kurfi ta bayyana cewa an soke aikin sakataren karamar hukumar da sufabaizeri kansalilo guda takwas na karamar hukumar.
Takardar wadda aka rubuta ta,a ranar 15 ga watan afrilu 2024, ta bada shelan cewa an dakatar da aikin nasu ne, domin karamar hukumar tana son fuskantar sabon tsari da yanayi a na sabon cigaba.
An gode ma wadanda aka dakatar da aikin nasu da kuma yi masu fatan Alheri. Takardar ta tabbatar babu wani laifi da aka same su dashi, kuma sunyi aiki tsakani da Allah a lokacin da suke rike da mukaman su.
Binciken jaridun Katsina Times ya tabbatar cewa a duk kananan hukumomin 34 dake jahar Katsina, karamar hukumar kurfi ce kadai tayi wannan aikin.
Me ya kawo wannan kora ko saukewa daga aiki? Wadanda da aka sallama sun fada ma jaridun Katsina Times cewa, da yawansu a kafar sadarwar zamani suka ga wannan sakon, babu wani zama da akayi dasu domin a fada masu dalilin daukar wannan matsayi akan su, a matsayin Wanda aka yi shekaru biyu ana aiki dasu cikin biyayya da mutunci.
Sun ce kwatsam suka ji labari kamar mafarki. Wasu ma da aka fada masu sukayi ta karyatawa, sai da aka tabbatar masu ta aiko masu da takardar dake yawo a "social media"
Da yawansu sun fada ma jaridun Katsina Times cewa har yanzu suna a cikin girgiza na abin da akayi masu.
Sun fada cewa suna da harkokin da ya kamata a biya su, ba fada masu ba, shin za a biya su ? Kuma yaushe?
Binciken da Katsina Times tayi ta gano sallamar kansilolin da sakataren karamar hukumar, bai Saba ma wata dokar aiki ba, don haka ba wata doka da aka Saba.
Duk binciken da jaridun Katsina Times tayi na gano dalilin wannan kora ta kasa samun kwakwkwaran hujja, amma an fi danganta lamarin da wani gasar siyasa da kuma fadan ruwan sanyi dake ruruwa tsakanin Bangarori
biyu na siyasa a karamar hukumar ta kurfi.
Bangare daya, shine na Dan majalisar tarayya mai wakiltar kurfi da Dutsinma Alhaji Aminu Balele Dan arewa. Daya kuma Bangaren shine na shugaban ma aikatan gidan gwamnatin Katsina, Alhaji Jabiru tsauri, Lamidon Katsina.
Binciken Katsina Times ya gano kowane Bangare yana son tabbatar da ikon shi a tasirin karamar hukumar. Ana zargin shugaban karamar hukumar ta kurfi, Wanda ada Babban yaron Dan arewa ne na siyasa a kurfi, yanzu yana karkatawa zuwa wajen Jabiru tsauri.
Zargi mai karfi na cewa wannan fadan siyasa na manya shine ya tafi da kujerun sufabaizari kansilolin da kuma sakataren karamar hukumar.
07043777779