KOTU TA TABBATAR DA TSAGIN DAVID MARK A SHUGABANCIN ADC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, a matsayin shugaban jam'iyyar ADC, in da ta kori karar da wani Dan Majalisar Wakilai,…

Katsina City News July 02, 2026  ·  12:00 AM
| 78 Views
KOTU TA TABBATAR DA TSAGIN DAVID MARK A SHUGABANCIN ADC
KOTU TA TABBATAR DA TSAGIN DAVID MARK A SHUGABANCIN ADC


Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, a matsayin shugaban jam'iyyar ADC, in da ta kori karar da wani Dan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, ya shigar ya na kalubalantar tsarin shugabancin jam'iyyar.


A sa'ilin da Mai Shari'a Musa Liman ke yanke hukuncin, ya bayyana cewar karar ba ta da wani tartibin nasibi, sannan kuma ta shafi batutuwan cikin gida ne na jam'iyyar ta ADC.


Mai Shari'a Musa Liman ya zartar da cewa Leke Abejide ya gaza tabbatar da cewa an tauye wani hakki na shi na shari'a a sakamakon samar da shugabancin jam'iyyar na yanzu.


Ya kuma kara da cewa Dan Majalisar Wakilan bai bi matakan warware rashin fahimta na cikin gida na jam'iyyar ba, gabanin ya shigar da wannan kara.


Advertisement

Kamar yadda Kotun ta bayyana, kotuna ba su da hurumi a cikin batutuwan da su ka shafi tsare-tsaren shugabanci na cikin gida na jam'iyyu , face idan ya kasance an sabawa doka ko kuma an tauye wasu hakkoki na ya-yan jam'iyyun wanda doka ta ba su.


Daga nan sai kotun ta zartar da cewa chanjin shugabancin ADC daga Nwosu zuwa David Mark bai sabawa kudin tsarin mulkin jam'iyyar ADC ko kuwa dokar zabe ba.


Sannan kuma Mai Shari'a Liman ya tabbatar da cewa taron ma su ruwa da tsaki da a ka gudanar a ranar 2 ga watan Yuli na shekara ta 2025, kafin babban taron Kwamitin Zartarwa na ranar 29 ga watan Yuli na shekara ta 2025, wani bangare ne na halatattun shirye-shirye da su ka samar da David Mark a matsayin Shugaban ADC na kasa, da Rauf Aregbesola a matsayin Sakataren Jam'iyyar na kasa.


Alkalin babbar kotun ya lura da cewa an gudanar da taron a gaban wakilin Hukumar Zabe, wanda hakan ya tabbatar da halaccin taron.


Daga nan sai ya tabbatar da cewa, samuwar David Mark da Aregbesola a matsayin shugabannin jam'iyyar ya tafi daidai da tanaje-tanajen tsarin mulkin jam'iyyar ADC, da kuma tanaje-tanajen dokar zabe

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 8 + 1?