Zainab Abubakar: Matar da Mijinta ya gudu ya barta da 'Ya'ya 4, Al'umma sun nuna Jinƙai
- Katsina City News
- 21 Aug, 2023
- 1055
Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina Times
A ranar Asabar da ta gaba aka wayi gari da wani abin tausayi na wata Mata mai suna Zainab Abubakar a kafafen Sada Zumunta na Zamani, Bidiyon da yayi yawo matuka ya nuna Matar da Yaranta 4 Mata 2 da Maza 2, Sai ita Mahaifiyar tasu da ke fama da ciwon Ƙafa.
Katsina Times ta Tuntuɓi ɗaya daga cikin wadanda bidiyon ya fito ta hannunsu kasantuwar bayyana Lambar waya da sukai don neman taimako bisa ga irin halin da matar take ciki, inda ya bayyana mana gaskiyar bidiyon da kuma karin bayani.
Matar mai suna Zainab Abubakar wadda dukkanin uaran nata guda biyu suka kamu da ciwon yunwa, ta tsinci kanta a cikin wani mawuyacin hali sanadiyyar Mijinta da ya gudu ya barsu a gidan Haya.
Mijin nata ya gudu ya barta a gidan haya inda ya zuwa hada wannan Rahoto ba'asan inda yake ba. Ita kuma ta cigaba da yawon bara don neman abinci, a haka wani mai Direban Babur (Dan'achaɓa) ya Ture ta har ta samu karaya a ƙafa, wanda hakan yayi sanadiyar zamanta a gida.
Zainab Bakuwa ce bata da Dangi a garin Katsina hakan ya janyo 'Ya'yanta Masu ƙarancin shekaru suka kamu da ciwon yunwa sanadiyyar ƙarancin Abinci, ga halin rashin lafiya da mahaifiyarsu take ciki.
Yaɗuwar Video keda wuya sai al'ummar ciki da wajen Katsina suka nuna halin tausayi inda suka ci-gaba da aiko da gudunmawa zuwa ga Matar, inda har tsohon Danmajalisar tarayya daga Katsina Hon. Sani Aliyu Danlami yace "Zai Dauki Nauyin kula da lafiyarta har ta warke" Hon Aliyu Abubakar Albaba, shima daga Katsina ya je kuma ya bada gudunmawa.
Al'umma daban-daban da kungiyoyi kowa ya bada tasa gudummawar, a inda Gwamnatin jihar Katsina itama ta shiga cikin Lamarin Malama Zainab Abubakar dake kwance Asibiti don karbar Magani.
Mi ya biyo bayan wannan?
Wasu bata gari 'Yan Damfara sun fake da halin da wannan mata take ciki suna Damfarar Mutane da sunan Tallafawa Matar da 'Ya'yanta, wanda har wasu suke ganin yakamata a dakatar da kaimata gudunmawa saboda Gwamnati ta shiga cikin al'amarin, inda wasu kuma suke ganin ya dace a ci-gaba da taimakonta kuma a samar mata gidan zama duba da gidan haya take zaune.
Koma dai mi kenan, Al'umma sun nuna halin jinkai wanda yakamata kuma Akwai ire-iren Zainab Abubakar dake cikin irin wannan mawuyacin hali da suke buƙatar Taimako wanda da al'umma zasu bincika kuma suyi Don Allah da an taimakawa da yawa daga mabukata.