KARIN HASKE:TALLAFIN HATSIN DA KANANAN HUKUMOMI KE RABAWA —

top-news



Daga Maiwada DanMalam

Biyo bayan korafe korafe a dandalin yanar gizo na Fesbuk kan cewa tallafin masara da gwamnati ta umurci a raba a fadin jiha don tallafa ma talakawa, cewa masarar bata da kyau, wannan rubutu  jan hankali ne ga al’ummar Jihar Katsina don a fahimci yadda abin yake. 

  Tallafin da aka tsara bayarwa ga jama a,kashi biyu ne. Akwai wanda Gwamnatin Jiha ta umurci Kananan Hukumomi su saya su raba ma mutanen su, akwai kuma wanda Gwamnatin Tarayya ta bada umurnin aba kowace Jiha N5bn su saya, su raba ma al’ummar Jihohin su, daga baya su biya cikin shekaru biyu.

Tallafin hatsi na naira bilyan biyar  da ya fito daga Gwamnatin Tarayya, wannan har yanzu ma kudaden basu shigo hannun gwamnatin Jihohi ba. 
Kenan, ba’a kai ga saye ba ballantana har a sayi mara kyau a raba ma al’umma. 

Tallafi na biyu kuma wanda Jihar Katsina ta umurci Kananan Hukumomi su saya su raba, wannan kowa yaji jawabin Maigirma Gwamna ranar da akayi taron addu’o’i, inda ya bayyana cewa Kananan Hukumomi ne zasu saya  da kan su, su raba ma al’umma, har ya jaddada cewa amana ne ce ya damka masu kuma suji tsoron Allah su sauke amanar yadda yakamata. 

Kenan, ba Gwamnatin Jiha bace ta bada kwangilar sayen hatsin ga wani mutum ba wanda za’a ce yayi yadda yake so, ya kawo hatsin da bai da kyau. Kowace Karamar Hukuma ita ta sawo hatsin ta ta kuma raba. Ma’ana, babu yadda za ace duka Kananan Hukumomi 34 dake a Jihar Katsina wuri daya suka je suka sayi hatsin kuma duka suka kasa gane rubabbe ne. Kowace da inda ta sawo nata. 

Wannan ba yana nufin ba’a samu matsala a wasu wurare kamar yadda wasu sukayi korafi ba. Haka kuma, ba yana nufin an samu ba. Zuwa yanzu dai babu wani koke mai ingantattar hujja da aka kawo ma Gwamnatin Jihar Katsina kan haka. Kenan, akwai bukatar wadanda ke da hujjar wannan matsalar su rubuto tare da sanar da Gwamnati inda aka samu matsalar don a bincika aji inda matsalar take a dauki mataki. 

Akwai bukatar al’umma su rika yi ma gwamnati kyakkyawan zato, su kuma zama idanun gwamnati wajen aiwatar da kudurori da manufofin ta na inganta rayuwar al’umma a fadin Jihar Katsina baki daya. Yakamata al’umma su zama masu adalci ga gwamnati ta hanyar tabbbatar da matsala da kuma yadda take kafin a fara zargin rashin kyautawa. Idan aka duba wannan dambarwar, tana iya yiwuwa an samu matsala a wata Karamar Hukuma ko wani bangare na Karamar Hukumar. Kenan, bai dace ayi kudin goro ace duka hatsin da aka sawo ne yake da matsala kamar yadda wasu Ke kokarin nunawa ba. 

A karshe, ina kira da mu fahimce cewa sai mun taimaka ma gwamnati tare da bata hadin kai wajen sauke nauyin da aka dora mata kafin a samu nasarar da ake nema. Kofar Gwamnatin Jihar Katsina a bude take wajen karba da duba koken al’umma don yin maganin matsalolin da suka dame su. Duk mai ingantattar hujja akan wannan matsala ko wata wadda ta shafi al’umma yana da ikon rubutawa ya hada tare da hujjojin shi, gwamnati zata kalli abin ta kuma dauki mataki. 

Allah Ya saukaka ma al’umma saukin rayuwa tare da ciyar da Jihar Katsina gaba. 

Maiwada Dammallam
DG Media