Katsina Times
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da sauya mukaman mashawarta na musamman guda biyu domin ƙarfafa aiwatar da manufofi da inganta ayyukan gwamnati.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jiha, Abdullahi Garba Faskari, ya fitar a ranar 23 ga Afrilu, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa an mayar da Abubakar Ahmed Tsanni daga Sashen Matasa da Wasanni zuwa Sashen Ci gaban Al’umma, yayin da Nasiru Ahmed Mulumfashi ya tashi daga Sashen Raya Karkara da Walwalar Jama’a zuwa Sashen Matasa da Wasanni.
A cewar sanarwar, sauyin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na ƙara ƙwarewa, kirkire-kirkire da inganci a harkokin mulki.
Ta kuma ce gwamnan ya nuna kwarin gwiwa cewa mashawartan za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen inganta muhimman manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa a sassan da aka tura su.
Haka kuma, gwamnan ya buƙaci su gudanar da aikinsu da jajircewa, gaskiya da kuma ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyansu ga gwamnati da al’ummar jihar.