’Yan sanda sun kama matashi kan zargin satar babur, an nemi ba su cin hanci a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22042026_060131_FB_IMG_1776837635650.jpg


KatsinaTimes 

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta cafke wani matashi mai suna Abdurra’uf Salisu, wanda aka fi sani da “Abdul Mai Dukiya”, mai shekaru 27, bisa zargin satar babur a cikin birnin Katsina.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, mazaunin rukunin gidajen Sardauna, ya aikata laifin ne tare da wani abokin aikinsa mai suna Abba, mazaunin unguwar Kerau, wanda a yanzu haka jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo.

Rahotanni sun ce ana zargin sun yi amfani da wani nau’in makulli da ake kira “master key” wajen satar babur din mallakin Isma’il Ibrahim, mazaunin unguwar Inwala a Katsina.

A yayin da ake ci gaba da bincike, wani mutum mai suna Mustapha Nasiru, dan karamar hukumar Rimi, ya kai wa jami’an bincike kudi har Naira 243,000, inda ake zargin ya yi yunkurin ba da cin hanci domin a saki wanda ake zargi.

Sai dai jami’an ’yan sanda sun ki karbar kudin, inda suka tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da bincike tare da daukar matakin doka kan duk masu hannu a lamarin.

Follow Us