HAJJI DA SHUGABANCI NA GARI KARKASHIN JAGORANCIN FARFESA PAKISTAN

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23112025_082905_IMG-20251117-WA0008.jpg

Rubutu na Musamman 
Daga 
Muhsin Tasi’u Yau

A yau, duniya ta zama wuri guda. Fasaha ta sauya yadda muke tafiya, yadda muke koyon abubuwa, da yadda muke gudanar da manyan ayyuka. Hajj, duk da kasancewarsa ibada ce mai dindindin tun zamanin Annabawa, ya zama wani babban tsari na zamani da ake gudanarwa cikin hanyoyi masu fasaha da tsarin gudanarwa na ƙwararru. A ƙasarmu Nijeriya, wannan sabon salo ya fara bayyana sosai a shekarun baya-bayan nan. Amma a ga sauyi tare da tasirinsa a qanqanin lokaci sai lokacin jagorancin shugaba na gari abin koyi Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan wanda ya tsaya tsayin daka don samar da shugabanci da ayyukan hajji mai tafe da zamani.
SABUWAR DUNIYAR HAJJ: TA FASAHA DA TSARI
Alhazai a yanzu ba sa buƙatar dogon takardu da fam-fam kamar da. Rajista da bayanai sun koma ta kan layi (online). Takardu, bayanan lafiya, jadawalin tashi, har ma da horon manasik, ana samun su a wayar hannu. Wannan sabon sauyi ya rage cunkoso, ya rage ruɗani, ya kuma taimaka wajen sauƙaƙa wa jama’a.
A tsahon shekara guda na zaman Farfesa Pakistan a shugancin hukumar, Hajj ya koma abu mai tsari sosai wanda ya haɗa gwamnati, kamfanonin jiragen sama, cibiyoyin kiwon lafiya, jami’an tsaro, da hukumomin Saudiyya. Wannan haɗin gwiwa na zamani ne ke tabbatar da cewa duk wanda ya shirya, zai iya tafiya cikin sauƙi.
DAGA GIDA ZUWA FILIN JIRGI: HORO DA TAIMAKO SUN SAUYA
Matakin farko na Hajj a yau yana farawa da horo ta zamani. Tsofaffi da matasa da maza da mata  duk suna samun bayanai ta WhatsApp, YouTube, rubutun bidiyo, da taron kai tsaye. Wannan ya rage tsoron da ake yi wa Hajj, musamman ga masu tafiya a karon farko. A filin jirgin sama kuma, alhazai na samun taimako kai tsaye. Ana taimaka musu da kaya, ana nuna musu hanyoyi, ana gyara musu takardu, ana tabbatar da jin dadin su kafin tashi.  A nan ma an samu sauyi sosai a qa ake ganin yadda aikin Hajj ya sauya daga tsarin gargajiya zuwa tsarin zamani, mai cike da kulawa da bin ka’ida. 
ZUWA SAUDIYYA: KULAWA A MATAKI-MATAKI
Da zarar alhazai sun isa Saudiyya, tsarin zamani ya ci gaba da aiki. Motoci, masauki, jadawalin manasik  komai yana bi ta tsarin da aka tsara tun daga gida. Jami’ai su na nan a kowane lokaci domin warware matsaloli cikin gaggawa. A ƙasashen da jama’a ke da yawa irin tamu, tsarin ya zama mafi muhimmanci. Domin inda ake tafiyar da dubban mutane lokaci guda, sai an yi aiki cikin tsari kamar yadda ake yi wajen manyan taron duniya. Duk da haka, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya yi matuqar qoqari don ganin alhazan Nijeriya ba su fuskanci kowacce irin matsala ba.

FASAHA TA SAUYA RAYUWAR ALHAZAI
Zamani abokin tafiya . Wannan ma’aikatar a qarqashin jagorancin Prof Pakistan Akwai abubuwan zamani da alhazai suka ci gajiyarsa a lokacinsa. Misali:
Aikace-aikacen wayar hannu don neman hanya,
Taswirar masauki da motoci,
Labaran lokaci-lokaci ta sakon waya,
Tsarin gaggawa domin magance matsalolin lafiya,
Jerin laccoci da bidiyo na koyon manasik.
Wannan sabuwar fasaha ta sa Hajj ya zama mai sauƙi fiye da baya, musamman ga matasa masu son fahimtar komai cikin hanzari.

JAGORANCI A ZAMANIN YANZU: BA MULKI  SAI HIDIMA
Halin mutum jarinsa. Sannan amfanin ilimi aiki da shi. Ba sai an tsawaita bayani ba, duk wanda ya san shugaban hukumar alhazai ta qasa Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya san malami ne mai tawadhi’u da son jama’a da yi musu hidima a kan kansa bare kuma in an wakilta shi. Wannan ta sa tunda aka ba shi wannan jagorancin bai zauna ba har sai da ya tabbatar an yi aikin hajji lafiya da nutsuwa an kammala lafiya. Haka cikin girmamawa da mutunta juna.  A zamanin da muke ciki, jama’a musamman matasa na kallon jagoranci ta wani sabon fuska. Jagora na zamani shi ne wanda yake sauka kasa, yana tattaunawa, yana lallashi, yana sauraro, yana gyarawa. Ayyukan Hajj sun zama wata hanya da ake ganin irin wannan jagoranci wanda ke ba da kulawa ga kowa, ba tare da nuna bambanci ba. Bayan haka, aikin Hajj yana buƙatar jagoranci mai natsuwa, wanda ke iya yin aiki da manyan hukumomi, kasashe, da dubban mutane a lokaci guda. Wannan yana nuna irin ƙwarewar da ake buƙata wajen gudanar da harkokin al’umma a zamanin yau. Shakka babu in ana buqatar hoton wannan jagora to shi ne Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan
KAMMALAWA
“Hasken Hajj a Zamaninmu” na nuni da yadda aikin Hajj ya sauya, ya tsaru, ya zamanantu, kuma ya ci gaba da bayar da darasi ga kowa. Ya nuna cewa addini ba tare da tsari ba yana iya zama wahala, kuma zamani ba tare da mutunci da ibada ba zai rasa tushe. Don haka wajibi ne a jinjinawa wannan shugaban hukumar Alhazai ta qasa (NAHCON) Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan. 
Hajj ya zama haɗin kai ne tsakanin tsohon tarihi da sabuwar fasaha. Ya zama alamar yadda muke tafiya daga gida zuwa ƙasa mai tsarki cikin kulawa, tsaro, natsuwa, da fahimta. Wannan hasken ne ya ke canza yadda ake gudanar da Hajj a wannan lokacin shugabancin Farfesa Pakistan kuma shi ne hasken da zai ci gaba da haskaka gaba.

Follow Us