Kungiyar Dikko Project Movement Ta na Maraba da Zuwan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima a Jihar Katsina
Kungiyar Dikko Project Movement, ƙarƙashin jagorancin Hon. Musa Gafai, ta bayyana maraba da zuwan Mai Girma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, wanda zai kai ziyara a jihar Katsina a ranar Talata, 21 ga Oktoba, 2025, domin ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan ci gaba da Gwamnatin Jihar Katsina ta aiwatar.
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa wannan ziyara wata babbar dama ce ga al’ummar jihar Katsina domin ganin irin ci gaban da Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ke aiwatarwa a fannoni daban-daban na rayuwa.
Kungiyar ta kuma yi kira ga jama’ar jihar Katsina da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tarbar Mataimakin Shugaban Ƙasa da nuna masa kauna da goyon baya.
Haka kuma, kungiyar ta yaba wa Gwamna Dikko Radda bisa jajircewarsa wajen aiwatar da ayyukan ci gaba da suka shafi ilimi, noma, lafiya, da inganta tattalin arzikin jihar.
Daga Dikko Project Movement.