NUJ Jihar Katsina Ta Taya Farfesa Sani Lugga Murnar Samun Sarautar Wazirin Ilimin Ƙasar Hausa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08092025_232325_FB_IMG_1757373692772.jpg



Daga Wakilinmu, Katsina Times

Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Katsina ta kai ziyarar taya murna ga Farfesa Sani Abubakar Lugga, MFR, bisa samun sarautar Wazirin Ilimin Ƙasar Hausa da Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji (Dr.) Umar Faruq Umar, CON ya tabbatar masa a lokacin bikin Sallar Gani da aka gudanar a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal, bisa al’adar masarautar ta Daura.

Ƙungiyar ta je ziyarar ne da yammacin Litinin 8 ga watan Satumba 2025, ƙarƙashin jagorancin Shugaban ta na Katsina, Comrade Tukur Hassan Dan’ali, domin nuna farin ciki da girmamawa ga sabon matsayi da Farfesa Lugga ya samu daga masarautar.

Da yake jawabi a wajen, Comrade Dan’ali ya bayyana cewa Farfesa Lugga uba ne ga Ƙungiyar NUJ da mambobinta, don haka suka ga dacewar zuwa don nuna farin ciki da wannan karramawa.

“A matsayinka na uba ga wannan Ƙungiya, ya dace muzo mu nuna farin ciki da wannan sarauta da Mai martaba Sarkin Daura ya ba ka. A madadin mambobin NUJ na Katsina, muna taya ka murna tare da jinjinawa ga masarautar Daura bisa wannan karamci,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa NUJ ta gode wa Farfesa Lugga bisa irin addu’o’i da shawarwarin da yake ba wa ‘yan jarida a kullum.

“Muna godiya da irin addu’a da shawarwari da kake yi mana. Muna fatan wannan sabon matsayi zai ƙara ƙarfafa ka wajen ci gaba da taimaka wa al’umma baki ɗaya,” in ji Dan’ali.

A nasa jawabin, Farfesa Sani Lugga ya nuna farin ciki da wannan ziyara, tare da bayyana dalilan da suka sa masarautar ta Daura ta ga dacewar ba shi wannan sarauta. Ya ce ya gudanar da bincike mai zurfi kan tarihin masarautar Daura da alakar ta da ƙasashen waje, musamman Turkiyya, inda ya gabatar da takarda ta musamman ga Mai martaba Sarki.

“Na gudanar da bincike na tarihi game da masarautar Daura da dangantakarta da wasu ƙasashen waje, ciki har da Turkiyya. Na fitar da muƙala da na gabatar wa Mai martaba, wadda ya yaba sosai har ya shirya tattaunawa da manyan jami’an fada. Daga nan ne ya ga dacewar ba ni wannan sarauta, ba wai don neman kaina ba, sai don cancanta,” in ji shi.

Ya gode wa Sarkin Daura bisa wannan karramawa, tare da yi wa Ƙungiyar NUJ da sauran al’umma fatan alheri da addu’a.

“Ina yi muku fatan alheri, kuma Allah ya albarkaci aikin jarida da kuke yi na faɗakarwa da ilmantar da al’umma,” ya ƙara da cewa.

Ziyarar ta ƙare da fatan alheri, addu’o’i, da kuma ƙarfafa zumunci tsakanin NUJ da Farfesa Lugga.

Follow Us