KatsinaTimes
Babban Mataimaki na Musamman a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina kuma tsohon dan majalisar dokokin jihar, Hon. Jabiru Yusuf Yau Yau, ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin Dikko Umaru Radda.
A wata wasikar murabus da ya aike wa Gwamnan ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar (SGS) a ranar Alhamis, 14 ga Agusta, 2025, Jabiru Yusuf ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne saboda dalilan kansa.
Ya gode wa gwamnan bisa damar da ya ba shi na yin aiki a cikin gwamnatinsa, yana mai bayyana wannan damar a matsayin wata babbar kyauta da ba zai taɓa mantawa da ita ba.
“Da girmamawa, na gode da taimako da kokarin da kuka yi wajen saka ni cikin gwamnatin ku, wanda wata babbar dama ce a gareni, kuma ba zan taɓa mantawa da ita ba a rayuwata, tun lokacin da kuka girmama ni a lokacin gwamnatin ku,” in ji shi a cikin wasikar.
Tsohon hadimin ya yi addu’ar fatan alheri ga Gwamna Radda, gwamnatin jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya, tare da roƙon a amince da murabus ɗinsa.