Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), reshen Kano, ta gurfanar da jami’an Hukumar Tara Haraji ta Jihar Katsina guda biyar tare da wani ma’aikacin banki a gaban Mai Shari’a Musa Danladi na Babbar Kotun Jihar Katsina, kan zargin wawure kudaden haraji na sama da naira biliyan 1.2.
Wadanda aka gurfanar sun hada da, Nura Lawal, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim Mamman, Abubakar Saidu, Rabiu Adamu Abdullahi da Adam Alhassan Albashir (ma’aikacin First Bank).
Ana zargin su da hada baki da karkatar da kudaden haraji da suka kai naira biliyan 1.235 da aka samu daga kungiyoyin kiwon lafiya irin su WHO, Médecins Sans Frontières da ALIMA, kudin da aka ce ya kamata su kai ga gwamnatin jihar Katsina.
Binciken EFCC ya nuna cewa Rabiu Abdullahi wanda shi ne tsohon Daraktan Tara Haraji kuma yanzu Sakatare na dindindin, shi ne ya amince da bude wani asusun banki a sunan BOIRS a Sterling Bank. Daga nan ne aka nada wasu jami’an hukumar haraji a matsayin masu sa hannu su kadai a asusun, kuma aka rika tura kudaden zuwa kamfanin NADIKKO General Suppliers, mallakin Nura Lawal.
Kudaden da aka sace an gano su a asusun banki daban-daban na wadanda ake tuhuma.
Duk wadanda ake tuhumar sun musanta laifin da ake zarginsu da shi. Lauyoyin su sun nemi belinsu, sai dai lauyan EFCC, Musa Isah, ya kalubalanci bukatar.
Bayan sauraron hujjojin bangarorin biyu, mai shari’a Danladi ya bayar da beli ga kowanne da sharadin biyan naira miliyan 5, da kawo mai tsaya musu wanda ke da kadarar fili a yankin kotun. An dage sauraron shari’ar zuwa 27 ga Oktoba, 2025