Wani sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Jihar Legas, bayan da wasu mambobi suka fito fili suna neman cire shugaban jam’iyyar na jiha, Fasto Cornelius Ojelabi, bisa zargin nuna son kai da gazawar shugabanci.
Rikicin ya samo asali ne daga yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwani na jam’iyyar kafin zaɓen ƙananan hukumomi da aka kammala kwanan nan, da kuma rikicin shugabanci da ya dabaibaye Majalisar Dokokin Jihar a baya-bayan nan.
A ranar Lahadi ne Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi guda 57, wato na kananan hukumomi 20 da kuma yankunan ci gaba na ƙananan hukumomi (LCDAs) guda 37, wanda hakan ya haifar da ƙarin zazzafar muhawara a cikin jam’iyyar.
A ranar Litinin, wasu masu zanga-zanga da suka fito ƙarƙashin Concerned and Loyal APC Members suka mamaye titunan Legas, suna zargin shugabancin jam’iyyar da nuna bambanci da fifita wasu a cikin nade-naden mukamai, musamman daga ɓangaren Justice Forum (JF).
Sun ce Fasto Ojelabi ne ke da alhakin gazawar jam’iyyar a zaɓen ƙananan hukumomi na 2025, tare da rashin iya tafiyar da harkokin jam’iyya yadda ya kamata.
Masu zanga-zangar, waɗanda suka fito daga dukkanin LGAs da LCDAs na jihar, sun taru a gaban Majalisar Dokoki ta Legas suna ɗauke da takardu da alluna, tare da faɗin wakoki na adawa da shugaban jam’iyyar. Wannan ya sa jami’an tsaro suka bazu a wurin domin tabbatar da doka da oda.
Wata majiya daga cikin jagororin jam’iyyar ta bayyana cewa rikicin ya raba kawunan manyan jiga-jigan jam’iyyar da ke cikin Governance Advisory Council (GAC), inda wasu daga cikinsu suka koka da cewa an kau da su wajen yanke shawarar nade-naden sabbin shugabannin kananan hukumomi.
Shugaban masu zanga-zangar, Segun Faleye, ya karanta takardar koke da suka mika wa Gwamna Sanwo-Olu, inda suka nemi a gaggauta cire Ojelabi daga shugabancin jam’iyyar.
"Roƙonmu ga shugabannin jam’iyyarmu shi ne su umurci Fasto Ojelabi ya sauka daga kujerarsa YANZU, domin kaucewa wata gagarumar matsala da ka iya ɓullo wa cikin harkokin gudanarwar jam’iyyar," in ji takardar.
Haka kuma, masu zanga-zangar sun bukaci a bar masu rike da muƙaman tsarin mulki su gudanar da aikinsu ba tare da tsoma baki daga masu son zuciya ba.
A nasa martanin, mai magana da yawun jam’iyyar APC a Legas, Seye Oladejo, ya tabbatar da zanga-zangar, yana mai cewa hakan wani salo ne na bayyana ra’ayi cikin lumana. Ya kuma ce duk wani nadi ko nade-naden da za a yi zai bi ƙa’idodin jam’iyya tare da shawarwari daga shugabannin.
"Jam’iyya ba za ta lamunci ƙoƙarin tilasta wasu nade-nade ba. Za mu bi tsarin da ya dace domin tabbatar da adalci," in ji shi.
A yayin rantsar da shugabannin kananan hukumomin ranar Lahadi, Gwamna Sanwo-Olu ya haramta musu naɗa sakatarorin ƙananan hukumomi da kuma kwamishinonin gudanarwa na wucin gadi har sai gwamnatin jiha ta bada izini. Ya bukace su da su mai da hankali wajen kula da bukatun al’umma a cikin kwanaki 30 zuwa 60 masu zuwa.